Matawalle VS Lawal: Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Manyan Yan Takara 2 a Jihar Zamfara
3 - tsawon mintuna
A ranar Asabar, 18 ga watan Maris ne al’ummar jihar Zamfara za su fito kwansu da kwarkwatarsu domin zabar wanda suke so ya jagorance su a matsayin gwamna na tsawon shekaru hudu masu zuwa.
A wannan zauren, Legit.ng Hausa ta zakulo maku wasu muhimman abubuwa da ya kamata ku sani game da manyan yan takara biyu da ke neman kujerar gwamnan Zamfara a zaben 2023.
Gwamna Bello Matawalle na neman zarcewa a kan kujerarsa a karo na biyu karkashin inuwar jam’iyyar APC yayin da Dauda lawal ke neman kujerar a inuwar PDP.
Muhammad Bello Matawalle na APC
- An haifi Muhammad Bello Matawalle a ranar 12 ga watan Fabrairun 1969 a yankin Maradun da ke jihar Zamfara.
- Ya yi karatunsa na Firamare a garin Maradun inda ya mallaki satifiket dinsa a shekarar 1979.
- Matawalle ya kammala karatunsa daga VTC Bunza a 1984. Ya kuma halarci kwalejin kimiyya ta Yaba da ke Lagas inda daga bisani ya tafi jami’ar Thames Valley da ke Landan.
- Ya yi aiki a matsayin malamin makaranta a kwalejin mata da ke Moriki da Kwatarkoshi kafin ya koma ma’aikatar albarkatun ruwa ta tarayya.
- Matawalle ya shiga harkar siyasa a 1998 lokacin da ya nemi kujerar dan majalisa kuma ya yi nasara karkashin rusasshiyar jam’iyyar United Nigeria Congress Party (UNCP).
- Tsakanin 1999 da 2003, ya yi aiki a matsayin kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta, kwamishinan muhalli da raya karkara da kwamishinan matasa da wasanni duk a jihar Zamfara.
- An zabi Matawalle domin ya wakilci mazabarsa ta Bakura/Maradun a majalisar wakilai a watan Mayun 2003 karkashin jam’iyyar All Nigeria Peoples Party (ANPP).
- An sake zabarsa a 2007 karkashin ANPP amma ya sauya sheka zuwa PDP wanda a cikinta ne aka sake zabarsa a karo na uku a 2011.
- A shekarar 2019, Matawalle ya yi takarar gwamna a karkashin jam’iyyar PDP amma ya samu kuri’u 189,452 yayin da dan takarar APC Muktar Idris ya samu 534,541. Bayan ba dan takarar APC satifiket sai kotun daukaka kara ta nemi a janye.
- Kotun koli ta ayyana Matawalle wanda ya zo na biyu a matsayin zababben gwamna bayan ta soke zaben APC.
- Matawalle ya sauya sheka daga jam’iyyarsa ta PDP a 2021 inda ya koma jam’iyyar APC mai mulki.
- Gwamnan na Zamfara na da matan aure guda hudu da ‘ya’ya da yawa.
- Shine dan takarar gwamnan jam’iyyar APC a jihar Zamfara a zaben ranar 18 ga watan Maris.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Dauda Lawal na PDP
- An haifi Dauda Lawal a ranar 2 ga watan Satumban 1965 a garin Gusau da ke jihar Zamfara.
- Lawal ya kammala karatunsa na digiri daga jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria a kimiyyar siyasa.
- Ya mallaki digiri na biyu duk daga jami’ar ABU sannan ya mallaki digirin digirgir daga jami’ar Usman Danfodiyo da ke Sokoto a bangaren kasuwanci.
- Ya fara aiki da Hukumar Kula da Hadin Kai da Tattalin Arziki ta Najeriya a shekara ta 1989.
- Ya koma aiki da kamfanin Westex Nigeria Limited a shekarar1989 a matsayin mataimakin manaja.
- Dauda Lawal ya yi takarar kujerar gwamnan jihar Zamfara a shekarar 2019 karkashin inuwar jam’iyyar APC.
- Dauda Lawal shine dan takarar gwamnan jam'iyyar PDP a jihar Zamfara a zaben 2023.
Asali: Legit.ng