Abinda Ya Sa Peter Obi Ya Shiga Takarar Shugaban Kasa, Keyamo Ya Fasa Kwai
- Ƙaramin ministan kwadugo, Festus Keyamo, ya ce Allah ya aiko Peter Obi ne domin maida Tinubu shugaban kasa
- Jigon jam'iyyar APC ya ce suna ganin girman Malaman Majami'u da ake ma wahayi amma sun yi kuskure a wannan karon
- Bola Tinubu ya samu nasara a zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairu, 2023
Abuja - Karamin ministan kwadugo da samar da ayyukan yi, Festus Keyamo (SAN), ya ce Allah ne ya ɗaga jam'iyyar Labour Party (LP) da ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi.
A wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Tuwita, Keyamo ya yi ikirarin cewa Allah ya ɗaga darajar Obi ne domin ya zama musabbin nasarar ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, Bola Tinubu.
A kalaman da ya wallafa, Keyawo ya ce:
"Lallai ne Allah ya turo Peter Obi ne bisa wani dalili, wannan dalilin ba komai bane illa ya zama sanadin maida Asiwaju Bola Tinubu shugaban ƙasa."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Peter Obi ya zo ne da nufin kawo karshe amma ba wai shi ne karshen zancen ba."
Da yake kara nuna farin cikinsa game da nasarar Tinubu, karamin minista a gwamnatin Buhari ya ce duk waɗanda suka yi tsammanin Obi zai lashe zaben shugaban ƙasa a watan Fabrairu, to sun yi kuskure.
A cewarsa mafi yawan bayin Allah da suka faɗi wahayin cewa tsohon gwamnan Anambra zai kai labari ranar 25 ga watan Fabrairu, lallai sun tafka kurkure a wahayin su.
Ministan ya ci gaba da cewa:
"Mafi yawan mutanen Allah (watau Malaman coci masu cewa an musu wahayi), muna matukar ba su girmansu, amma a zahirin gaskiya sun tafka kuskure a wahayin da suka gani game da zaɓen 2023."
Idan baku manta ba, Farfesa Mahmud Yakubu, shugaban INEC ya ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa bayan samun kuri'u mafiya rinjaye.
Jam'iyyar APC Ta Kori Tsohon Kwamishina
A wani labarin kuma Duk da Tinubu Ya Ci Zabe, APC Ta Kori Wani Babban Jigo Da Ta Gano Ya Mata Zagon Ƙasa
APC ta faitittiki tsohon kwamishinan hukumar sauraron korafin jama'a ta ƙasa bayan gano yana mata zagon ƙasa a jihar Imo.
Asali: Legit.ng