Shekarau: Dalilin Da Ya Sa Na Shiga Motar Gwamna Ganduje

Shekarau: Dalilin Da Ya Sa Na Shiga Motar Gwamna Ganduje

  • Malam Ibrahim Shekarau ya bayyana cewa haduwarsa da Gwamna Ganduje a baya bayan nan bata da alaka da siyasa
  • Tsohon gwamnan na Kano ya ce sun hadu da gwamnan ne a wajen jana'izar abokin su kuma ya roki da zai raka shi gida
  • Shekarau ya bayyana cewa ba shi da matsala da duk jagororin Kano, kuma yana maraba da duk wanda yazo don su tattauna cigaban jihar

Jihar Kano - Tsohon gwamnan Jihar Kano, Senator Ibrahim Shekarau, ya fayyace bayani kan haduwar sa da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a baya bayan nan, Daily Trust ta rahoto.

An yi ta yamadidi da zancen tun bayan da Ganduje ya raka Shekarau gidansa bayan sun halarci sallar jana'izar attajirin dan kwangila, Alhaji Sani Dahiru Yakasai, a fadar sarki, ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Rai Bakon Duniya: Allah Ya Yiwa Shahrarren Dan Kwangila a Jihar Kano, Alhaji Sani Dahiru Yakasai, Rasuwa

Ganduje da Shekarau
Abin da ya sa na shiga motar Ganduje, Shekarau. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Yayin da wasu masu sharhi su ke alakanta lamarin da siyasa, wasu na ganin cewa Shekarau zai iya umartar magoya bayansa da su zabi jam'iyyar APC da dan takarar ta, Nasir Gawuna, a zaben gwamnoni na ranar Asabar.

Sai dai, a wata tattaunawa da gidan rediyon Faransa (rfi), Shekarau wanda dan jam'iyyar PDP ne kuma daya daga cikin daraktocin yakin neman zaben jam'iyyar a zaben da ya gudana, ya ce haduwar bata da alaka da siyasa.

Ya ce akwai kyakkyawar alaka tsakanin sa da sauran jagororin jihar, ya kara da cewa sun sha haduwa da sauran jagorori, harda Senator Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar NNPP.

Ya ce:

''Zancen gaskiya, mun hadu ne a wajen ta'aziyyar abokin mu, Alhaji Sani Dahiru Yakasai. Mun hadu a wajen sallar jana'iza da ta gudana a fadar sarki. Bayan an idar da sallah, mun je makabarta a motarsa. Bayan an binne gawa, gwamnan ya rike hannuna ya ce dole sai ya karasa abin da ya fara, shi ne ya mayar da ni har gida.

Kara karanta wannan

"Ta Ji Min Rauni A Maraina": Dan Chinan Da Ya Kashe Ummita Ya Bayyanawa Kotu

''Sai nayi masa godiya muka kuma tafi gidana tare. Babu batun siyasa a nan. Kawai dai abu ne akan gaba. Ba mu da wata babbar matsala. Muna girmama juna. Kamar dai Kwankwaso, muna haduwa sosai a filin jirgin sama mu kuma gaisa ayi wasa da dariya da juna."

Da ya ke jawabi kan ko sunyi ganawar rufe kofa da gwamnan, Shekarau ya ce, ''to kuna so mu bar kofa a bude lokacin ganawa? Bamu yi zancen da ya shafi siyasa ba. Muna magana ne akan rasuwar wannan mutum da kuma yadda rayuwar mu za ta kasance.''

Ya ce kofarsa a bude ta ke don tattaunawa da kowa da ya zo wajensa, ya kara da cewa ba zai rufe kofa ga kowanne dan siyasa ba in dai yazo wajensa don su tattauna cigaban jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164