Jam'iyyar APC Ta Kori Tsohon Kwamishina Bayan Gano Yana Mata Zagon Kasa
- Jam'iyyar APC a jihar Imo ta kori tsohon kwamishinan hukumar korafin jama'a ta ƙasa, Willie Amadi, daga inuwarta
- Mambobin kwamitun zartaswa na gundumar babban jigon ne suka ɗauki wannan matakin kan zargin da ake masa
- An tuhumi babban jigon da hannun a yi wa jam'iyyar zagon ƙasa da kuma shiga harkokin cin amana
Imo - Jam'iyyar APC mai mulki ta kori babban jigonta kuma tsohon kwamishinan hukumar sauraron korafe-korafen al'umma ta ƙasa, Barista Willie Amadi.
Shugabannin APC na gundumarsa Ikenegbu Ward 1, ƙaramar hukumar Owerri Municipal, jihar Imo ne suka kori jigon bisa zargin da ya shafi cin amanar jam'iya.
Mista Amadi, masanin doka kuma Lauya, wanda ya fi shahara a harkokin siyasa, shi ne maƙasudin kafa kwamitin bincike da jam'iyyar APC ta yi don gano gaskiya.
The Nation ta tattaro cewa wasiƙar kora daga inuwar APC da aka aike wa Amadi tana ƙunshe da sa hannun mambobin 28 ciki har shugaban jam'iyya na gunduma, Chuka Ihejieto, da Sakatare, Chidiebere Emeribe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wani sashin takardan ya ce:
"Amadi na da hannun wajen yaudarar jagororin APC, kashe musu kasuwa da yaɗa labaran karya, haka nan yana wasu harkoki da nufin durkusad da jam'iyya."
"Bisa haka shugabannin gunduma suka zauna suka yi nazari kan batutuwa da dama da shawarin kwamitin ladaftarwa, sun yanke korar Willie Amadi saboda ya saɓa wa sashi na 21.2, i, ii, iii, vii, viii na kundin dokokin APC."
Labarin korar Barista Amadi daga APC ya baiwa da yawan mutane mamaki, wasu magoya bayan jam'iyyar sun nuna rashin jin daɗi da fushinsu game da matakin da jagororin suka ɗauka.
Sai dai a wata sanarwa da kakakin APC, Chidiebere Emeribe, ya fitar, ya ce jam'iyyar ba ta da wani zaɓin da ya wuce haka duba da tuhume-tuhumen da ake masa.
Manyan yan takara biyu a jihar Buhari
A wani gefen kuma mun tattara muku Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Yan Takarar Gwamna 2 a Katsina
Bayan tsaikon da aka samu sakamakon saita na'urorin BVAS, INEC ta ce ranar 18 ga watan Maris zata gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya.
Jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin da APC ke mulki amma ana ganin tana da babban kalubale a gabanta.
Asali: Legit.ng