NNPP Ta Kori Dan Takarar Mataimakin Gwamna da Shugabanni a Katsina
- Jam'iyyar NNPP ta yanke hukunci kan manyan kusoshinta da suka ayyana goyon baya ga Dikko Raɗɗa a Katsina
- Kakakin NNPP na jihar, Usman Kankiya, ya ce matakin ya haɗa har da ɗan takarar mataimakin gwamna, Rabe Darma
- A cewarsa, jam'iyyar ta dauki wannan matakin ne kan zargin cin amana kuma zasu saurari NNPP ta ƙasa ta amince
Katsina - Jam'iyyar NNPP mai kayan marmari reshen jihar Katsina ta tsige ɗan takarar mataimakin gwamna, Muttaqa Rabe-Darma, shugaban jam'iya da sauran jagororin jiha.
Jami'in hulɗa da jama'a na jam'iyyar NNPP, Nasiru Usman-Kankia, ne ya bayyana haka ga manema labarai ranar Jumu'a a Katsina, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.
Ya ce NNPP ta ɗauki wannan matakin ne saboda gano suna mata zagon ƙasa, ciki har da goyon bayan dan takarar gwamna a inuwar APC, Dakta Dikko Raɗda.
Usman Kankiya ya ce:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Kamar yadda kuka samu labari, wani bangaren shugabannin NNPP sun kira taro ba kan ƙa'ida ba ranar Alhamis 9 ga watan Maris, suka yanke shawarin da ya girgiza jam'iyya."
"A taron, wanda ɗan takarar gwamnan APC ya halarta, an gabatar da shugaban NNPP na jiha, Liti, ɗan takarar mataimakin gwamna, Rabe Darma da wasu kusoshi a matsayin masu sauya sheka zuwa APC."
"Ana bayyana haka, nan take wurin ya hargitse da hayaniya, aka fara jin tashin taken NNPP daga bakin magoya baya kuma suka riƙa nanata a'a, a'a, a'a."
Ya ƙara da cewa nan take ɗan takarar gwamnan APC ya yi karin haske cewa ya tattauna batun haɗa kai da NNPP, amma ba wai sauya sheƙa ba.
Kakakin NNPP ya tunatar da cewa tun a ranar 5 ga watan Maris, sun gargaɗi mambobi, shugabanni da 'yan takara su guji kulla kawance da kowace jam'iyar siyasa.
Su wa NNPP ta kora daga inuwarta a Katsina?
"Taron gaggawan da muka kira ya yi nazari kana ya yanke matakin korar duk wanda ke da hannu a taron cin amana, yayin da zamu saurari amincewar shugabanni na ƙasa," inji shi.
Ya ce waɗanda aka kora sun haɗa da, shugaban jam'iyya, Sani Liti, Sakataren jiha, Umar Jibril, shugaban matasa, Mustapha Basheer, shugaban shiyyar Katsina, Dauda Kurfi da takawaransa na Funtua, Abdullahi Mai'adua.
Sauran su ne shugaban jam'iyya na shiyyar Daura, Dakta Sale Mashi, ɗan takarar mataimakin gwamna, Rabe Darma, da kuma Sanata Audu Yandoma, kamar yadda PM News ta rahoto.
A wani labarin kuma mun tattara maku Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Yan Takara 2 a Katsina
Nan da mako ɗaya tal, INEC zata gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya kuma Katsina na ɗaya daga wuraren da ake ganin sai APC ta yi dagaske.
Asali: Legit.ng