Yan Daba Sun Faramaki Ayarin Dan Takarar Gwamnan LP a Kaduna, Sun Raunata 4
- An shiga tashin hankali yayin da wasu tsagerun 'yan daba suka farmaki ayarin ɗan takarar gwamnan Labour Party a Kaduna, Jonathan Asake
- Mai magana da yawunsa ya ce lamarin ya auku lokacin da ake sallar Jumu'a a Gidan Waya, karamar hukumar Jema'a kuma maza 2 mata 2 suka ji raunuka
- Ya ce lokacin da ayarin tawagar kamfen ya zo wuce wa, ba zato yan daba suka fara jifa da duwatsu da sadduna, jami'an tsaro suka shiga tsakani
Kaduna - Wasu tsagerun 'yan daba sun kai hari kan ayarin kamfen ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna karƙashin inuwar Labour Party (LP), Honorabul Jonathan Asake, ranar Jumu'a.
Jaridar Ledership ta tattaro cewa yan daban sun kaddamar da hari kan Ayarin tawagar ɗan siyasan a ƙauyen Gidan Waya, ƙaramar hukumar Jema'a ta jihar Kaduna.
A wata sanarwa da mai taimakawa ɗan takarar gwamnan LP kan harkokin midiya, James Swam, ya fitar, ya ce matasa huɗu, maza biyu da mata biyu, ne suka ji raunuka.
A cewar Sanarwan lamarin ya faru ne yayin da Ayarin tawagar yakin neman zaɓen ya zo wuce wa ta Gidan Waya lokacin ana Sallar Jumu'a.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
James Swam ya ce tawagarsu na kan hanyar zuwa garin Godogodo da wasu garuruwa domin tallata ɗan takararta yayin da jirgin kamfen LP ya dira ƙaramar hukumar.
Ya ƙara da cewa bayan motoci uku sun yi nasarar tsallake Tayoyin da aka sanya don toshe Titin, ba zato 'yan daban suka fara ruwan duwatsu, sanduna da wasu abubuwa ma su cutarwa kan Ayarin.
"Har sai da jami'an tsaron da ke tare da ɗan takarar gwamnan suka shiga tsakani, sannan aka samu nasarar daƙile rikicin," inji Mista Swam.
Yan takarar gwamna 2 a Katsina
A wani labarin na daban kuma Mun haɗa muku Muhimman Abubuwan Da Ya Kamata Ku Sani Game Manyan 'Yan Takarar gwamna 2 a Katsina.
A ranar 18 ga watan Maris, 2023, za'a gudanar da zaben gwamnoni a Najeriya kuma jihar Katsina na ɗaya daga cikin jihohin da fafatawa zata yi zafi tsakanin mutum biyu.
Jam'iyyar APC na kokarin ci gaba da jan zarenta jihar yayin da babbar jam'iyyar hamayya PDP ke fatan kwace mulkin Katsina ya koma hannunta.
Asali: Legit.ng