Jigo a jam'iyyar APC Daga Arewa Yayi Kira a Bawa Kirista Daman Zama Shugaban jam'iyyar APC
- Tun bayan zaben shugaban kasa jam'iyyar APC take kokarin fito da salo na lallabar wadanda aka batawa biyo bayan takarar tikitin Muslim-Muslim na APC
- Da fari taso tayi amfani da yawan yan majalisar ta wajen dannan kirjin yan kudu da kujerar shugaban majalisar dattawan Najeriya
- Yau kuma jigo a jam'iyyar yayi kira ga shugaban jami'iyyar APC Sanata Adamu, da yayi murabus domin bawa kirista daman shugabancin jam'iyyar
Kamar yadda aka sani zaɓe shugaban ƙasa dana Sanatoci yazo ya tafi yabar baya da ƙura.
Da alama dai, ƙurar ce yanzu masu ruwa da tsaki keta daman ganin sun warware domin gudun shiga yanayin la-ila-hula'i.
Son ɗinke irin wannan ɓarakar ce tasa, mataimakin shugaban jam'iyyar APC a arewa maso yamma Salihu Lukman yace kamata ki yayi ace kirista ne zai maye gurbin Abdullahi Adamu, shugaban jam'iyyar APC na ƙasa.
2023: Cikin Gwamnan PDP Mai Neman Tazarce Ya Kaɗa, Babbar Jam'iyyar Adawa Ta Koma Bayan Ɗan Takarar APC
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Salihu Lukman, ya bada hujja da cewa, hakan na da kyau duba da yadda zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Bola Tinubu da Kashin Shettima suke Musulmi.
Idan za'a iya tunawa, gabanin zaben da aka yi na shugaban ƙasa, wannan batu na ɗaya daga cikin manyan batutuwa da suka ja hankali wanda yasa jam'iyyar mai mulki ta rasa mabiyanta da yawa zuwa ga jam'iyyun adawa.
A wani saƙo daya aikewa manema labarai a juma'ar nan, Lukman yace, dole ne a tsarin shugabancin jam'iyyar APC a dama da kowa.
A cewar sa:
"... Shugabancin jam'iyya yayi aiki mai kyau wajen ganin yazo da ɗan takarar da yayi nasara a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 duk da ƙalubale da aka fuskanta, hakan abune mai kyau da bazai hana Sen. Adamu ya ajiye kujerar sa ta shugabancin jam'iyyar APC domin bawa Kirista dama suma su ɗanɗana," Inji shi.
"Domin haka ta faru, akwai buƙatar taron jam'iyya na gaggawa. A tsari magajin Adamu zai kasance Sanata Abubakar Kyari ne wanda shima musulmi ne daga Arewa maso gabas,"
Jaridar The Cable ta kuma ruwaito yadda ya kuma shawarci sakataren jam'iyyar na ƙasa, Iyiola Omisore daya ajiye kujerar sa saboda matsalar da zaɓen sa ta janyo daga tsagin jam'iyyar na jihar Osun.
Dalilin Da Yasa Ƙawancen Da PDP Ta Yi Da Wasu Jam'iyyu 9 A Kaduna Baya Ɗaga Min Hankali - Uba Sani
Ɗan takarar gwamna na jihar Kaduna, Uba Sani, ya sanar da cewa bai damu da kawancen da jam'iyyar PDP ta yi da wasu jam'iyyun siyasa 9 a jihar ba.
Uba Sani ya ce jam'iyyun ba a san su ba, kuma mutanen Jihar Kaduna za su zaɓi sabon gwamna ne bisa ayyukan da ya yi a baya.
A cewar Sani, Isah Ashiru, dan takarar gwamna na PDP, ya shafe shekaru 8 a majalisar tarayya amma bai taɓa gabatar da kudirin doka ko daya ba.
Asali: Legit.ng