Zaɓen Gwamnoni: Jihohi Biyar Da APC Zata Iya Shan Kaye a Hannun PDP, NNPP Da Labour Party
A yayin da ake tunkarar zaɓen gwamnoni a Najeriya, jam'iyyar All Progressives Congress (APC) tana da jihohi 21 yayin da jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) take da jihohi 14, ciki har da wacce ta samu kwanannan,
Jihar Osun (wacce kotu zata yanke hukunci akan ta)
Jiha ɗaya da ta yi saura, Anambra, tana a hannun jam'iyyar All Progressives Grand Alliance (APGA )
Sai dai, akwai yiwuwar a samu sauyi a wasu jihohin, inda jam'iyyar APC zata iya rasa wasu jihohin ga PDP da sabuwar jam'iyyar nan mai tashe ta Labour Party, idan har za ayi la'akari da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.
Jerin jihohin dake nan ƙasa za su iya suɓucewa daga hannun jam'iyyar APC a zaɓen gwamnoni dake tafe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Jihar Kano/NNPP
Duba da yawan masu kaɗa ƙuri'ar dake a jihar Kano, APC zata so jihar ta cigaba. da kasancewa a hannun ta. Sai dai jam'iyyar za ta sha wuya wajen tabbatuwar hakan.
A zaɓen shugaban ƙasa da akayi, NNPP tayi lilis da APC a jihar. Idan ba wani sauyi aka samu ba, tarihi na iya sake maimaita kan sa a zaɓen gwamna.
2. Jihar Legas/Labour Party
Bayan shekaru masu yawa yana iko akan siyasar jihar Legas, a wannan karon jihar tana iya suɓucewa daga hannun zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
3. Jihar Katsina/PDP
Jihar Katsina nan ne mahaifar shugaban ƙasa Muhammadu Buhari. Amma a kan idon sa jihar ta suɓucewa zuwa hannun PDP a zaɓen shugaban ƙasa.
Jam'iyyar PDP zata iya kwace mulkin jihar Katsina idan akayi la'akari da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.
4. Jihar Kaduna/PDP
Duk da ƙarfin ikon da gwamna Nasir El-Rufai yake da shi a jihar, APC ba tayi abin a zo a gani ba a zaɓen shugaban ƙasa dana ƴan majalisun tarayya na ranar 25 ga watan Fabrairu.
Jam'iyyar ba wai kasa cin zaɓen shugaban ƙasa kaɗai tayi ba, ta rasa dukkanin kujerun sanatocin da take da su a jihar a hannun PDP.
5. Jihar Plateau/LP
Duk da cewa jihar Plateau tana a yankin Arewa ta Tsakiya, Peter Obi, shine ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a jihar.
Ɗan takarar gwamnan LP a jihar, Patrick Dakum, ka iya zama gwamnan Plateau, idan har an sake maimaita irin sakamakon zaɓen da aka samu a zaɓen shugaban ƙasa.
Tsohon Ɗan Takarar Gwamnan PDP Ya Sauya Sheƙa Zuwa APC a Jihar Neja
A wani labarin na daban kuma, jam'iyyar APC tayi wani babban kamu a jihar Neja.
Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar na jam'iyyar PDP ya sauya sheƙa zuwa cikin ta.
Asali: Legit.ng