PDP Ta Kori Sanata Nnamani Mai Yi Wa Tinubu Kamfe, Ta Kwace Tikitin Takararsa

PDP Ta Kori Sanata Nnamani Mai Yi Wa Tinubu Kamfe, Ta Kwace Tikitin Takararsa

  • Jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta kori tsohon gwamnan jihar Enugu, Sanata Chimaroke Nnamani daga jam'iyya a hukumance
  • Sanata Nnamani, gabanin babban zaben shugaban kasa na 2023, ya yi fice wurin nuna goyon bayansa a fili ga dan takarar jam'iyyar hamayya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
  • A cikin wasikar korarsa, jam'iyyar ta kuma ce an janye zabensa da aka yi a matsayin dan takarar sanata na Enugu ta gabas

Kwamitin ayyuka na kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ta sanar da korar Sanata Chimaroke Nnamani na Enugu ta gabas daga jam'iyya.

Kamar yadda jaridar New Telegraph ta rahoto, an tabbatar da korar sanatan ne cikin wasikar da jam'iyyar ta aike wa Hukumar zabe mai zaman kanta na kasa, INEC.

Chimaroke Nnamani
An alakanta korar Nnamani da goyon baya da ya ke yi wa Bola Tinubu a fili. Hoto: Photo: Senator Chimaroke Nnamani
Asali: Facebook

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kara karanta wannan

Gwamnan Bauchi: Duk da Yana PDP, Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai Ya Ayyana Goyon Baya Ga Dan Takarar APC

An kuma tattaro cewa baya ga korarsa daga jam'iyya, wasikar ta kuma ce Sanata Nnamani ba shine dan takarar yankin Enugu ta gabas a zaben da ke tafe ba.

A wani wasikar daban da shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Sanata Iyorchia Ayu ya fitar, an jadada cewa an kori Sanata Nnamani daga jam'iyya.

Sanata Ayu, a cikin wasikar, ya kuma sanar da INEC janye zabensa a matsayin dan takarar sanata na PDP a Enugu ta gabas.

Wasikar ta ce:

"Mun rubuta ne don sanar da ku cewa PDP, bisa ikon da kudin tsarin jam'iyya ya bata (da aka yi wa kwaskwarima a 2017) ta kori Sanata Chimaroke Nnamani a matsayin mambanta daga ranar Juma'a 10 ga watan Fabrairun 2023.
"Bayan korarsa, Sanata Nnamani ba dan jam'iyyar bane, kuma ya rasa zaben da daukan nauyinsa a matsayin dan takarar jam'iyyar a zaben sanata na Enugu ta gabas a babban zabe da ke tafe."

Kara karanta wannan

Afenifere Ta Yi Watsi Da Nasarar Tinubu, Ta Bayyana Dan Takarar Da Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Dr Ayu ya jadada cewa jam'iyyar ba ta da dan takarar sanata a Enugu ta gabasa a babban zaben 2023.

"Yayin da muke fatan samun hadin kai daga gare ku; kamar ko da yaushe, muna muku fatan alheri."

DSS sun kama wasu jiga-jigan PDP uku a Kaduna kan zargin 'shirin tada zaune tsaye' yayin zabe da ke tafe

A wani rahoron kun ji cewa yan sandan farin kaya na DSS sun kama, Sa'idu Adamu, mataimakin shugaban kwamitin kamfe na dan takarar gwamnan Kaduna na jam'iyyar PDP.

An kama shi tare da Talib Mohammed da El-Abbas Mohammed, shugabannin matasa na PDP kan zargin shirin tada fitina yayin zaben gwamna da yan majalisu da ke tafe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164