Kotu Ta Yanke Hukunci Kan Yin Amfani Da Katin Zaɓe Na Wucin Gadi Ranar Zaɓe
- Wata kotu ta yanke hukunci kan yin amfani da katin zaɓe na wucin gadi a yayin zaɓen dake tafe
- Kotun tayi umurni ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta bar wasu tsirarun mutane suyi amfani da shi
- Hukuncin kotun dai ba kowa da kowa ya shafa, inda kotun ta sahalewa waɗanda kawai suka shigar da ƙarar ne suyi amfani da katin zaɓen na wucin gadi
Abuja- Wata babbar kotun tarayya a birnin tarayya Abuja, a ranar Alhamis, ta umurci hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta bari ayi amfani da katin zaɓe na wucin gadi (TVC) a zaɓen gwamnoni da na ƴan majalisun jiha.
Mai shari'a Obiora Egwuatu, ya bayar da umurnin yayin da yake yanke hukunci kan ƙarar da wasu fusatattun mutum biyu suka shigar suna neman a bar su suyi amfani da katin zaɓen na wucin gadi tunda basu da na din-din-din.
Alƙali Egwuatu yace ya bayar da umurnin ne saboda masu shigar da ƙarar sun yi rajista sannan akwai bayanan su a matattarar bayanai ta hukumar INEC. Rahoton Daily Trust
"An bayar da umurnin dole ga wanda ake ƙara (INEC) ta bar waɗanda suka shigar da ƙarar su yi amfani da katin zaɓen su na wucin gadi wajen yin zaɓe." Inji alƙalin
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Hukuncin wannan kotun ya biyo bayan cewa masu ƙarar sun cike dukkanin sharuɗɗan yin rajista kuma akwai bayanan su a wajen INEC, saboda haka suna da yancin yin zaɓe ta hanyar yin amfani katin zaɓe na wucin gadi a zaɓen 2023."
Hukuncin Bai Shafi Sauran Masu Katin Wucin Gadi Ba
Sai dai, alƙalin ya bayyana cewa ba zai iya amsa musu roƙon su na uku ba, wanda shine a bari duk wani wanda ya cancanci kaɗa ƙuri'a mai katin zaɓe na wucin gadi yayi amfani da shi, saboda ƙarar ba a shigar da ita ta gama gari ba. PR Times
Gaskiya Ta Fito Fili, INEC Ta Bayyana Dalilin Dakatar Da Zaɓen Tambuwal Da Sauran Ƴan Majalisun Tarayya a Sokoto
“Wannan ƙarar tun da bata gama gari bace, ba zan iya amsa buƙata ta uku da masu shigar da ƙarar suke nema ba."
Kotun tayi nuni da cewa babu wani waje na hurumin doka tun daga kunɗin tsarin mulki na shekarar 1999 da dokar zaɓe, wanda ya nuna cewa dole sai katin zaɓe na din-din-din za ayi amfani da shi."
"Amma doka ta bayar da hurumin yin amfani da katin zaɓe a sashi na 47."
Kotu Ta Garkame Tsohon Mataimakin Gwamnan Imo a Gidan Gyara Hali
A wani labarin na daban kuma, wata kotu ta tura tsohon mataimakin gwamnan jihar Imo gidan gyaran hali.
Kotun ta yanke wannan hukuncin ne bayan ta kammala sauraron bayanai daga ɓangarorin mai ƙara da wanda aƙe ƙara.
Asali: Legit.ng