Dan Takararmu Na Gwamna a Jihar Katsina Bai Janye Ba, Inji PDP

Dan Takararmu Na Gwamna a Jihar Katsina Bai Janye Ba, Inji PDP

  • Jam'iyyar PDP reshen jihar Katsina ta musanta jita-jitar da ke yawo cewa dan takarar gwamna ya janye daga takara
  • Kwamitin kamfen Yakubu Lado Ɗan Marke ya yi zargin cewa APC ce ta kulla labarin don ɓata wa dan takarar suna
  • Ya yi kira ga mutanen Katsina su yi watsi da takardan da ke yawo domin ba ta hito daga Ofishin Mustapha Inuwa ba

Katsina - Peoples Democratic Party (PDP) a jihar Katsina ta yi fatali da raɗe-raɗin da ke yawo cewa ɗan takararta na gwamna, Sanata Yakubu Ƙado Ɗanmarke, ya janye.

Shugaban sashin midiya na kwamitin kamfen PDP a jihar Katsina, Alhaji Kabir Yusuf-Yar’adua ne ya musanta jita-jitar a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.

Sanata Yakubu Lado Dan-Marke.
Dan takarar gwamnan Katsina a inuwar PDP, Yakubu Lado Hoto: PDP Campaign
Asali: UGC

Ya ce

"An jawo hankalin kwamitin yakin neman zaɓen PDP na jihar Katsina kan wani labarin ƙarya da ake yaɗawa cewa ɗan takarar gwamna ya janye daga tseren takara."

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Babbar Kotu Ta Tsige Ɗan Takara a Jihar Arewa Kwana 3 Gabanin Zabe

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

"Jam'iyyar PDP na farin cikin sanar da cewa labarin ƙarya ne kuma babu ƙanshin gaskiya a ciki. Ko ɗaya Daraktan Kamfen Lado, Dakta Mustapha Inuwa, bai saki wata wasiƙa mai dauke da tambarin PDP ba."
"Kwamitin kamfe yana da kalar takardarsa ta daban da ake fitar da sanarwa a ciki. Saboda haka kwamitin kamfen PDP na baiwa mutane shawarin su yi watsi da sanarwan ta ƙarya."

Shin su wa PDP ke zargi da kitsa labarin?

Alhaji Yar'adua ya yi zargin cewa raɗe-raɗin wani shirin APC ne na ɓata wa ɗan takarar PDP suna a idon mutane saboda tana ganin yana ƙara karbuwa a lungu da saƙo.

A sanarwan, Alhaji Kabir Yar'Adua ya ci gaba da cewa:

"Ina tabbatar muku cewa ɗan takarar gwamnan PDP na nan a cikin masu neman mulkin Katsina, ko da yammacin nan na karbi daruruwan magoya bayan LP da suka amince zasu goya masa baya."

Kara karanta wannan

DSS Ta Kama Mambobin Jam'iyyar PDP 3 A Kaduna 'Kan Shirin Tada Rikici' Yayin Zaben Gwamna Da Majalisun Jiha

Ya ƙara da cewa Lado ya karbi bakuncin Malami da ma'aikatan manyan makarantun Katsina, wanda suka yi alkawarin mara masa baya.

A wani labarin kuma Hukumar INEC Ta Dage Zaben Gwamnoni da Yan Majalisun Jihohi Da Mako Ɗaya

A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun kwamishinan INEC na kasa, Festus Okoye, hukumar ta ce ba haka ta so amma ya zama wajibi ta ɗaga zaben.

INEC ta ce bayan hukuncin Kotu, zai ɗauke ta tsawon lokaci kafin ta gama saita na'urorin BVAS kuma ta maida su jihohi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262