Yan Takarar Gwamna Uku Sun Janye, Sun Marawa PDP Baya a Nasarawa

Yan Takarar Gwamna Uku Sun Janye, Sun Marawa PDP Baya a Nasarawa

  • Jam'iyyun siyasa da yan takarar su na gwamna sun rushe zuwa cikin jam'iyar PDP a Jihar Nasarawa
  • 'Yan takarar gwamnan 4 ciki har da jam'iyyar Labour Party sun janye daga tsere sun mara wa takwaransu na PDP baya
  • A cewarsu ya zama wajibi su kulla wannan kawance domin ceto jihar daga hannun APC mai mulki

Nasarawa - 'Yan takarar gwamna da jam'iyyunsu sun rushe tsarinsu domin mara wa babbar jam'iyyar hamayya PDP baya a jihar Nasarawa, kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.

Jam'iyyun siyasar da 'yan takararsu na gwamna sun cimma wannan matsaya ne a wata yarjejeniya da suka rattaɓawa hannu da yammacin ranar Laraba.

Taswirar Nasarawa.
Yan Takarar Gwamna Uku Sun Janye, Sun Marawa PDP Baya a Nasarawa Hoto: vanguardngr
Source: UGC

Sun amince su haɗa karfi da karfe domin kawar da gwamnatin jam'iyyar APC da kuma tabbatar da nasarar jam'iyyar PDP a zaben gwamnan Nasarawa da ke tafe.

Kara karanta wannan

DSS Ta Kama Mambobin Jam'iyyar PDP 3 A Kaduna 'Kan Shirin Tada Rikici' Yayin Zaben Gwamna Da Majalisun Jiha

Bayan cimma matsayar, ɗan takarar gwamna na LP, Joseph Ewuga, takwaransa na jam'iyyar AA, Asha Manga, na jam'iyyar NRM, Alhaji Musa Sambo da na jam'iyar ARP, Muhammed Auwal, suka janye daga takara.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

'Yan takarar guda huɗu sun janye daga tseren domin goyon bayan takwaransu na jam'iyyar PDP, Dakta David Ombugadu, ya zama gwamna a jihar Nasarawa.

Da yake jawabi ga 'yan jarida jim kaɗan bayan cimma matsayar janyewa a ƙauyen Danka, ƙaramar hukumar Lafiya, Joseph Ewuga, a madadin takwarorinsa ya ce ƙulla kawancen ya zama wajibi.

Ya ce ya zama tilas su haɗa kai su goyi bayan ɗan takarar jam'iyar PDP, David Ombugadu, domin ceto Nasarawa daga hannun jam'iyyar APC mai mulki, kamar yadda Sahara Reporters ta rahoto.

Gamayyar 'yan takarar gwamnan guda hudu sun roki ɗaukacin magoya bayansu a lungu da sako na jihar Nasarawa su zaɓi David Ombugadu na jam'iyar PDP a zaben gwamnan da ke tafe ranar Asabar.

Hukumar INEC Ta Dage Zaben Gwamnoni da Yan Majalisun Jihohi

Kara karanta wannan

Ta Kwaɓe, Yar Takarar Mataimakin Gwamna Ta Yi Murabus, Ta Koma APC da Dubbannin Mambobi

A wani labarin kuma Hukumar INEC ta ɗaga zaben gwamnoni da na yan majalisun jihohi da mako ɗaya

Zaben wanda ta tsara gudanarwa ranar 11 ga watan Maris, 2023 yanzu ya koma ranar 18 ga watan Maris, 2023.

A wata sanarwa da INEC ta fitar da yammacin Laraba, ta bayyana babban dalilin da ya tilasta mata kara mako guda.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262