'Yar Takarar Mataimakin Gwamnan SDP Ya Yi Murabus, Ya Koma APC a Legas
- Kwana uku gabanin fafata zaben gwamna a jihar Legas, jam'iyyar APC ta samu babban ƙarin goyon baya
- Yar takarar mataimakin gwamna da dandazon masoyanta sun sauya sheka zuwa APC mai mulki
- A cewarta bai kamata mutanen Legas su yi wasa da wannan damar da nasu ya zama shugaban kasa ba
Lagos - 'Yar takarar mataimakin gwamna a inuwar jam'iyyar SDP a jihar Legas, MIisis Abeni Animasahun, da dubannin magoya bayanta sun sauya sheƙa zuwa APC.
Ta kuma ayyana cikakken goyon baya ga takarar gwamna Babajide Sanwo-Olu ta neman tazarce, ta ce tawagarta zasu yi aiki ba kama hannun yaro don ya samu nasara, kamar yadda The Nation ta rahoto.
A wurin bikin tarban masu sauya shekar da aka shirya a Legas, tsohuwar yar takarar mataimakin gwamnan ta ce:
"Mun ɗauki wannan matakin ne bayan nazari kan dukkan masu neman kujerar gwamna har da na jam'iyyarmu, kama daga gogewarsu, kwarewar sanin aiki da karbuwarsu a wurin jama'ar Legas."
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Mun gano haɗin Sanwo-Olu da Dakta Quadri Hamzat ya kere tsara kuma ba bu wanda ya kamo ko da kafaɗarsu."
'Yar siyasan ta ce mutanen jihar Legas ba zasu watsar da ɗumbin nasarorin da wannan gwamnati mai ci ta samu a zangon farko saboda fushin siyasa ba, kamar yadda Vanguard ta rahoto.
Misis Animasahun ta yi nuni da wasu manyan ayyuka da gwamnan ya zuba wa talakawansa kama daga ayyukan walwala, inganta ilimi, kiwon lafiya, muhalli, tallafawa matasa, Sufuri, gidaje, kimiyya da fasaha da sauransu.
Ta ci gaɓa da cewa, "Zai kyautu matuka Legas ta yi amfani da damar da ta samu a hannu ta gwamnatin Asiwaju Ahmed Tinubu, ta cimma abubuwa da yawa."
"Kaɗa kuri'a ga Sanwo-Olu tamkar amincewa ne da ci gaban ayyuka na gari, amma Legas tana da muhimmancin da ba zamu kuskura mu miƙa ta hannun gurbatattun yan siyasa ba."
INEC Ta Soke Zabe a Mazabar Shugaban Masu Rinjaye
A wani labarin kuma INEC ta yi amai ta lashe, ta soke sakamakon zaben mamban majalisar tarayya a mazaɓar Doguwa/Tudun Wada.
Tun da fari baturen zaben yankin ya ayyana shugaban masu rinjaye a majalisar wakilan tarayya, Al-Hassan Ado Doguwa a matsayin wanda ya samu nasara.
Amma a sabon jawabin da ya yi a shalkwatar INEC, Farfesa Ibrahim Yakasai, ya ce sai an sakw shirya zabe a rumfuna 13.
Asali: Legit.ng