Zaɓen Gwamnoni: Jam'iyyar Labour Party Ta Musanta Haɗewa Da PDP a Jihar Kaduna
- Jam'iyyar Labour Party ta fito fili ta musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa ta marawa jam'iyyar PDP baya a zaɓen gwamnan jihar
- Jam'iyyar ta bayyana cewa an nemi ɗan takarar ta da ya janyewa ɗan takarar jam'iyyar PDP, amma ta ƙi amincewa
- Tayi kira ga magoya bayan ta da suyi watsi da labaran da ake yaɗawa cewa ta marawa PDP baya a zaɓen gwamnan jihar
Jihar Kaduna- Jam'iyyar Labour Party (LP) reshen jihar Kaduna tayi watsi da maganar cewa ɗan takarar gwamnan ta, Jonathan Asake, ya janye daga takara sannan ya koma marawa jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) baya.
A ranar Litinin ne dai ƴan takarar gwamna 9 suka koma bayan ɗan takarar PDP, Isah Ashiru Kudan, a yayin da ake tunkarar zaɓen gwamna a jihar.
Jam'iyyar Labour Party ta bayyana cewa an nemi ɗan takarar ta da ya janyewa Isah Ashiru, amma ta ƙi amincewa da hakan. Rahoton Daily Trust
Darektan shiryawa, bincike da tsare-tsare na jam'iyyar a jihar Kaduna, Dr Polycarp Gankon, shine ya bayyana hakan yayin tattaunawa da manema labarai a ranar Talata.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Ya bayyana cewa Asake har yanzu shine ɗan takarar da yafi cancanfa a cikin ƴan takarar zaɓen gwamnan jihar na ranar 11 ga watan Maris, 2023.
Ya bayyana cewa jam'iyyar LP tana kan turbar kare muradun Kudancin Kaduna sannan ba zata yarda da wani mataki wanda zai mayar da mutanen Kudancin Kaduna matsayin saniyar ware ba a jihar. Rahoton Leadership
A kalaman sa:
“Bayan shawarwari da tattaunawa da shugabannin jam'iyyar Labour Party a matakin jiha da na tarayya, da kuma duba da yanayin kaɗa ƙuri'un magoya bayan jam'iyyar a jihar Kaduna,
Muna faɗi da babbar murya cewa Labour Party ba zata yi wata haɗaka da PDP ba."
Daga nan kuma yayi kira ga magoya bayan su da suyi watsi da labaran kanzon kuregen da ake yaɗawa cewa jam'iyyar ta marawa PDP ko wata jam'iyya daban baya a jihar.
Obi Ya Soke Zuwa Kamfen Din Yan Takarar Gwamna, Yana Shirin Zuwa Kotu Ranar 8 Ga Watan Maris
A wani labarin na daban kuma, Peter Obi ya fasa zuwa kamfen ɗin ƴan takarar gwamna, zai garzaya kotu
Peter Obi dai shine babban jagoran jam'iyyar Labour Party (LP) a Najerya.
Asali: Legit.ng