Peter Obi Ya Fi Rabiu Kwankwaso Shahara a Jihohin Arewa 13

Peter Obi Ya Fi Rabiu Kwankwaso Shahara a Jihohin Arewa 13

  • Peter Obi na Labour Party ya samu yawan kuri'un da suka fi na Rabiu Musa Kwankwaso na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party a yankin arewa
  • Kafin zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, mutane da dama sun yarda cewa Kwankwaso ya fi Obi shahara a yankin
  • Sai dai kuma, bayan zaben, Peter Obi ya fi shi inda ya samu kuri'u 2,080,847 a fadin jihohin yayin da Kwankwaso ya samu 1,454,649

Kafin zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu, mutane da dama sun yi kira ga ayi maja tsakanin Peter Obi na Labour Party da Rabiu Musa Kwankwaso don yin tasiri sosai.

Sai dai kuma, dan takarar shugaban kasar na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) da Peter Obi sun gaza cimma matsaya guda kan wanda ya kamata ya zama ainahin dan takara da mataimaki.

Kara karanta wannan

Sabon Harin Zamfara Da Kano: Tinubu Ya Yi Allah Wadai, Ya Ce Dole a Takawa Kashe-Kashe Birki a Najeriya

Kwankwaso na ganin cewa shine ya fi Obi cancanta duba ga matsayinsa na wanda ke rike da digiri na uku, sanata, tsohon gwamna kuma ma'aikacin gwamnati, a bangarenshi Obi ya mallaki digiri na farko ne kawai.

Peter Obi da Kwankwaso, yan takarar shugaban kasar 2023
Peter Obi Ya Fi Rabiu Kwankwaso Shahara a Jihohin Arewa 13 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Sai dai kuma, da alama zaben ya kawo karshen komai game da dan takarar da ya fi shahara a tsakanin shugabannin biyu musamman a yankin arewacin kasar.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Obi ya samu kuri'u 2,080,847 a fadin jihohin arewa 19 yayin da Kwankwaso ya samu 1,454,649. Kwankwaso ya yi nasara ne a jiha daya kawai - mahaifarsa ta Kano.

Obi ya lashe jihohi biyu: Nasarawa da Filato.

Kusan kaso 75 na kuri'u miliyan 1.454 da Kwankwaso ya samu sun fito daga jihar Kano ne kawai.

Kwankwaso ya samu kaso 25 ne a jiha daya kawai, idan aka kwatanta da Obi wanda yya samu a jihohi hudu: Filato, Nasarawa, Benue da Taraba.

Kara karanta wannan

Tsakanin Atiku da Obi, Akwai Mai Karyar Shi Ya Lashe Zabe – Tsohon Shugaban APC

Obi ne na biyu a jihohin arewa biyu kuma na uku a jihohi bakwai, inda ya yi kasa da Kwankwaso a jihohi shida kawai.

Ga jerin jihohi 13 da Obi ya yi kokari fiye da Kwankwaso

  1. Kaduna
  2. Taraba
  3. Borno
  4. Gombe
  5. Kebbi
  6. Kogi
  7. Kwara
  8. Niger
  9. Sokoto
  10. Nasarawa
  11. Plateau
  12. Adamawa
  13. Benue.

Kungiyoyi sun fara kamun kafa don samun mukamai a gwamnatin Tinubu

A wani labarin kuma, mun ji cewa kungiyoyi daban-daban sun fara rage murya domin ganin sun samu mukaman siyasa a sabuwar gwamnati mai kamawa ta zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Tinubu.

Kungiyar Musulmai Mata ta Kasa wato FOMWAN ta yi kira ga Tinubu da ya kokarta ya baiwa mata kaso 50 cikin dari na mukamai a gwamnatinsa saboda rawar ganin da suka taka wajen nasarar da ya samu a zaben shugaban kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng