Jam'iyyar PDP Ta Karyata Jita-Jitar Gwamna Adeleke Zai Koma APC
- Jam'iyyar PDP ta musanta raɗe-raɗin da ake yaɗawa cewa gwamnan Osun na shirin sauya sheka zuwa APC
- A wata sanarwa da shugaban PDP na jihar ya fitar, ya ce labarin kirkirarre ne mara tushe balle makama
- A cewarsa nasarar PDP a jihar ranar zaben shugaban kasa kaɗai ta isa kuma zata maimata mako mai zuwa
Osun - Jam'iyyar PDP reshen jihar Osun ta musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa gwamna Ademola Adeleke na shirin tattara kayansa ya fice daga jam'iyar zuwa APC, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.
A wata sanarwa da shugaban PDP na jihar, Dakta Akindele, ya rattaba wa hannu kuma ya fitar a karshen makon nan, ya ce jita-jitar da ake yaɗawa a soshiyal midiya karya ce.
Ya ce labarin kanzon kuregen wanda APC ta kirkiro da nufin ɗauke hankalin mutane. Ya yi kira ga masu kaɗa kuri'a zu zabi PDP ranar 11 ga watan Maris.
Ya ƙara da cewa gwamna Adeleke na nan daram a PDP kuma ya shirya tsaf don yi wa jam'iyyar aiki kamar yadda kowa ya shaida a ranar zaben shugaban kasa da 'yan majalisun tarayya.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mista Akindele ya jaddada cewa PDP zata maimaita nasarar da ta samu ranar Asabar 11 ga watan Maris, 2023 ta hanyar lashe kujeru 26 na mambobin majalisar dokokin Osun.
Dailypost ta rahoto shugaban PDP na cewa:
"Ina kira ga ɗaukacin al'umma su yi fatali da jita-jitar sauya sheƙa, babu dalilin da zai sa haka ta faru musamman idan kuka yi la'akari ga nasarar PDP a zaben shugaban kasa da yan majalisu."
"APC a Osun ta ruguje tana fafutukar neman madafa, cikin kwanaki 100 da hawa mulki gwamna Adeleke ya nuna shugabanci na gari shiyasa mutane ke ta fatan alheri a lungu da saƙo."
"Saboda haka mutane su yi watsi da karyar da ake yaɗawa, gwamna Adeleke na nan daram a matsayin jagoran PDP na jihar Osun."
INEC ta fara ɗaukar matakai
A wani labarin kuma INEC Ta Haramtawa Wasu Mutane Shiga Zaben Gwamnoni, Ta Dauki Mataki Mai Zafi
Hukumar zabe ta ƙasa mai zaman kanta ta umarci REC su cire sunan duk ma'aikatan da suka yi sakaci a baya daga aiki a zaben gwamnoni mai zuwa.
Farfesa Mahmud Yakubu, shugaban hukumar na ƙasa ya ce sun shirya magance kalubalen da aka fuskanta a zaben da ya gabata.
Asali: Legit.ng