Gwamna El-Rufai Ya Fallasa Yadda Minista Ya Yaudari Buhari, Aka Canza Takardun Kudi
- Malam Nasir El-Rufai ya zargi Godwin Emefiele da kokarin taimakawa Jam’iyyar PDP a 2023
- Gwamnan jihar Kaduna ya ce tun farko ba Gwamnatin APC ta nada Emefiele ya rike CBN ba
- El-Rufai ya zargi Gwamnan babban banki da AGF da hannu wajen yaudarar Shugaban kasa
Abuja - Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yi maraba da hukuncin da kotun koli tayi a kan canjin kudin da gwamnatin tarayya ta fito da shi.
A wani gajeren bidiyo da yake dandalin Twitter, an ji Mai girma Nasir El-Rufai yana zargin Godwin Emefiele da fito da tsarin saboda a gurgunta PDP.
Gwamnan ya ce sanin asali ne ya jawo Gwamnan babban banki yake so jam’iyyar PDP ta karbe mulki domin tun farko a mulkinta ne aka nada shi.
A cewar tsohon Ministan na Abuja, an yaudari shugaba Muhammadu Buhari ne ya yarda da wannan tsari da ba a taba yi a wata kasa a Duniya ba.
Maganar Nasir El-Rufai
"Bari in fada cewa wannan tsarin (Godwin) Emefiele ne, Gwamnatin PDP ta nada Emefiele ya zama Gwamnan babban bankin CBN tun asali.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Saboda haka ka da mu manta da inda ya fito, kuma shi ya fito da wannan tsari domin ya taimakawa jam’iyyar PDP ta lashe babban zaben 2023.
Sai ya yaudari Shugaban kasa za a iya janye Naira Tiriliyan 2 daga hannun al’umma, ayi komai a watanni uku, babu kasar da ta taba yi a tarihi.
Ya yaudari Shugaban kasa ta hanyar ba shi bayanan karya, shi kuma babban lauyan gwamnatin tarayya ya goyi bayan tsarin, mun san dalili;
Ku je ku duba tarihinsu, mutane ne wadannan da suka nemi su shiga takarar kujerar Gwamna ko Shugaban kasa, amma ba su yi nasara ba.
- Malam Nasir El-Rufai
Talaka ya yi nasara a kotun koli
Malam El-Rufai yake cewa hukuncin da kotun koli ta zartar ya ba talaka damar ya shiga banki, ya bukaci a ba shi tsofaffin kudinsa da aka raba shi da su.
Da yake bayani tare da Yahaya Bello da Bello Matawalle a gefensa, El-Rufai ya nuna duk da mugun nufin da aka yi, jam’iyyarsu ta APC ta iya lashe zabe.
Shari'ar zaben Shugaban kasa
An samu labari ‘Dan takaran PDP, Atiku Abubakar ya ce shi ya lashe zabe, shi ma Peter Obi na LP ya ce shi ne wanda ya yi nasara a zaben da aka yi.
Tsohon Shugaban APC na kasa, Adams Oshiomhole ce ba za ta yiwu APC da LP suyi galaba a tare a lokaci daya ba, don haka a cikinsu akwai mai karya.
Asali: Legit.ng