Babban Jigon PDP Ya Yi Fatali da Okowa, Ya Koma APC Bayan Tinubu Ya Ci Zabe
- Wani babban jigon jam'iyyar PDP a jihar Delta ya sauya sheka zuwa APC jim kaɗan bayan sanar da Tinubu a matsayin wanda ya ci zaɓe
- Chief Aribogha Johnny ya ce komawarsa APC ba ta da alaƙa da nasarar Tinubu a zaben shugaban kasa
- Kwamitin kamfen ɗan takarar gwamnan Delta a inuwar APC ya tarbi babban dan siyasan hannu bibbiyu ranar Laraba
Delta - Fitaccen jigon jam'iyyar PDP a jihar Delta, Chief Aribogha Johnny, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a hukumance ranar Laraba tare da ɗumbin magoya bayansa.
Babban jigon PDP ya ɗauki wannan matakin ne awanni bayan INEC ta ayyana Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban kasa 2023.
A wata sanarwa da jaridar Punch ta ci karo da ita, tsohon jigon PDP ya ce komawarsa APC ba shi da alaƙa da sakamakon zaben shugaban kasa.
Mista Johnny ya ce:
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
"Ban ɗauki wannan matakin saboda sakamakon zaben shugaban kasa da aka kammala ba, na yi haka ne saboda wariya da nuna halin ko in kula da ake mun a PDP tsawon shekaru."
A cewarsa, yana tare da PDP tun tale-tale amma ya kama kansa ne daga lokacin da shugabannin jam'iyyar suka fara nuna masa wariya duk da rawar da ya taka har PDP ta kai ga nasara a Delta.
"Saboda haka naga ya dace na koma jam'iyyar da ake maraba da gudummuwa ta a siyasa kuma za'a rungume ni da yaba mun a matakin jiha da gaba," inji shi.
Yayin da suke maraba da sauya shekar Johnny, shugabannin APC a jihar Delta karkashin jagorancin daraktan kwamitin kamfen ɗan takarar gwamna sun nuna farin ciki kan ci gaban.
Sun tabbatar masa da cewa jam'iyyar APC zata ɗauke shi a matsayin wani babban ƙusa wanda za'a rika yanke hukunci tare da shi da magoya bayansa.
Gwamnan Gombe ya rasa kwamishina 1
A wani labarin kuma Kwamishina Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa Kwana 10 Gabanin Zaben Gwamnoni
Yayin da gwamnonin da ke neman tazarce ke ci gaba da haɗa kan mutane, lamarin ya sauya akala a jihar Gombe.
Ɗaya daga cikin kwamishinoni a Gombe ya yi murabus, ya ce naɗin da aka masa a takarda ne kawai amma babu wani abu da zai iya yi na taimakon mutane.
Asali: Legit.ng