Jam'iyyar NNPP Ta Nemi INEC Da Ta Soke Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 2023

Jam'iyyar NNPP Ta Nemi INEC Da Ta Soke Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 2023

  • Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP) ta caccaki yadda hukumar INEC ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasa
  • Jam'iyyar ta lissafo wasu abubuwa waɗanda take ganin bai kamata ace sun faru ba a zaɓen na bana
  • Daga ƙarshe sai ta nemi hukumar zaɓen data soke zaɓen shugaban ƙasan da aka gudanar a faɗin Najeriya

Abuja- Jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), tayi kira da soke sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023.

Jam'iyyar tayi wannan kiran ne a wani taron manema labarai da shugaban ta na ƙasa, Rufai Alkali, yayi a birnin tarayya Abuja. Rahoton Premium Times

Kwankwaso
Jam'iyyar NNPP Ta Nemi INEC Da Ta Soke Zaɓen Shugaban Ƙasa Na 2023 Hoto: Premium Times
Asali: UGC

Mr Alkali yace yadda INEC ta gudanar da zaɓen shugaban ƙasar, hukumar ta mayar da ƙasar nan baya wajen yin irin zaɓukan da akeyi kafin shekarar 2015.

“Mun damu matuƙa kan abubuwan da suka faru ranar zaɓe, hukumar zaɓen ta mayar da ƙasar mu baya wajen yin irin zaɓukan da akeyi kafin shekarar 2015, inda akeyin abinda aka ga dama, a hana masu kaɗa ƙuri'a zaɓe."

Kara karanta wannan

Shugaban APC Na Ƙasa Ya Caccaki PDP Da LP, Ya Tono Wata Maƙarƙashiyar Da Suke Ƙullawa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Satar akwatunan zaɓe, inda ake takurawa masu kaɗa ƙuri'a, siyan ƙuri'u da rigingimu sune abin da ke sanyawa a lashe zaɓe, inda jami'an tsaro suke komawa bayan jam'iyya mai mulki su taimaka tayi maguɗi a bainar jama'a."

Alkali ya lissafo wasu muhimman abubuwa bakwai da jam'iyyar su ta lura da su akan zaɓen sune, INEC da gangan ta hana NNPP sakewa a zaɓen, ta kyale shugaba Buhari da wasu yin kamfen ranar zaɓe, hana masu kaɗa ƙuri'a yin zaɓe,

Siyan ƙuri'u, lalacewar na'urar BVAS da aringizon ƙuri'u, ƙarya kan IREV da zaɓe wanda rigingimu suka yi yawa a cikin sa.

A dalilin haka, sai yayi kira da a soke zaɓen na shugaban ƙasa. Rahoton The Punch

"Domin ceto dimokuradiyyar mu da ƙasar mu, ƴan Najeriya da ƙawayenta dole ne su ƙi yarda da wannan sakamakon zaɓen."

Kara karanta wannan

"Na Daina Yin Zaɓe" Matashi Ya Fusata Ya Jefa Katin Zaɓen Sa Cikin Bola, Bidiyon Ya Yaɗu

"Saboda haka muna kiran da aka gaggauta dakatar da sanar da sakamakon zaɓen da soke zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a faɗin Najeriya. Sannan a gaggauta yin sabon zaɓe." Inji shi

Atiku da Peter Obi Sun Ki Sallamawa Bola Tinubu, Sun Fadi Matsayar da Za Su Dauka

A wani rahoton, Atiku da Peter Obi sun ƙi yarda da.sakamakon zaɓen shugaban ƙasa, wanda Bola Tinuɓi ya lashe.

Ƴan takarar sun bayyana mataki na gaba da za su ɗauka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng