An Gurfanar da Alhassan Ado Doguwa a Gaban Kotu Kan Zargin Kisa
- Hukumar 'yan sanda reshen jihar Kano ta gurfanar da ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Doguwa/Tundun Wada a Kotu
- Honorabul Ado Doguwa ya shiga hannu bisa zargin hannu a harin da ya yi ajalin mutane uku ranar zaben shugaban kasa
- A ranar Talata da ta shige ne jami'an tsaro suka yi ram da ɗan majalisar a filin jirgin Malam Aminu Kano
Kano - Hukumar 'yan sanda ta gurfanar da Al-Hassan Ado Doguwa, ɗan majalisar wakilan tarayya mai wakiltar Doguwa/Tundun Wada a gaban Kotu.
Daily Trust ta rahoto cewa an gurfanar da ɗan majalisar na APC ne bisa tuhumar hannu a kisan kan da aka yi a mazaɓarsa yayin zaben ranar Asabar.
A ranar Talata da ta gabata, jami'an tsaro suka cafke Doguwa a filin sauka da tashin jirgen sama na Malam Aminu Kano (MAKIA) bayan kashe mutum uku a yankinsa.
Jami'in hulɗa da jama'an na hukumar 'yan sandan Kano, SP Abdullahi Kiyawa, a wata sanarwa da ya fitar da safiyar yau Laraba, yace an kama Doguwa ne bayan ya ƙi amsa gayyata.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ya ce:
"Bayan samun korafin kashe wasu mutun uku da raunata wasu 8 a Tudun Wada ranar Asabar lokacin tattara sakamako da wani bidiyo dake yawo a soshiyal midiya, kwamishina ya ba da umarnin a gudanar da bincike."
"Yayin binciken, sashin binciken aikata muggan laifuka SCID ya tura gayyata ga Ado Doguwa ranar 27 ga watan Fabrairu, bisa zargin akwai haɗin bakinsa wajen aikata lamarin."
"Sakamakon ƙin amsa gayyatar, hukumar yan sanda ba ta da wani zabi da ya wuce kamo shi, shiyasa jami'an SCID dake Bampai, Kano suka yi ram da shi a filin Aminu Kano."
Kiyawa ya ƙara da cewa a halin yanzun hukumar yan sanda naci gaba da bincike kan lamarin kuma duk wanda ke da hannu nan gaba kaɗan zai shiga hannu, inji rahoton Premium Times.
Peter Obi Ya Yi Magana a Karon Farko Bayan Tinubu Ya Lashe Zabe
A wani labarin, Ɗan takarar Labour Party, Peter Obi, ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba zai yi wa yan Najeriya jawabi
Wannan na zuwa ne awanni kaɗan bayan hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa ta sanar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓe.
Asali: Legit.ng