Peter Obi Ya Yi Magana a Karon Farko Bayan Tinubu Ya Lashe Zabe
- A karon farko tun bayan ayyana Bola Tinubu a matsayin wanda ya samu nasara, Peter Obi ya faɗi shirinsa na gaba
- A wani gajeren sako da ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta, Obi ya ce nan gaba kaɗan zai yi wa yan Najeriya jawabi
- Hukumar zabe ta ƙasa watau INEC ta ayyana Bola Ahmed Tinubu na APC a matsayin zababben shugaban kasa
Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya yi alƙawarin jawabi kai tsaye ga 'yan Najeriya bayan INEC ta bayyana sakamakon zaɓen 2023.
Mista Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya faɗi haka ne a shafinsa na dandalin sada zumunta Tuwita ranar Laraba, 1 ga watan Maris, 2023.
Ya wallafa cewa:
"Yanzu haka ɗan takararmu na mataimakin shugaban kasa, Dakta Yusuf Datti Baba Ahmed, yana jawabi a wurin taron manema labarai na ƙasa da ƙasa a Hedkwatar LP da ke birnin tarayya Abuja."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ina shirin yin jawabi ga yan Najeriya da sauran ƙasahem duniya nan ba da jimawa ba."
Ku kwantar da hankula - Baba Ahmed
Da yake jawabi ga yan jarida a Abuja, abokin takarar Obi ya roki magoya baya su kwantar da hankulansu kana su maida hankali wajen tunkarar zaben gwamnoni ranar 11 ga watan Maris.
Datti Baba Ahmed ya roki duk wani masoyin Labour Party ya tabbata ya dangwala wa LP a zaben gwamnoni da yan majalisar jiha dake take.
Yayin da LP ta yi fatali da sakamakon zaben kuma magoya bayanta ke ikirarin an tafka kura-kurai, Baba Ahmed ya ce shugabansu zai yi jawabi nan ba da jimawa ba.
Amma ya tabbatar wa masoya cewa zasu ɗauki matakin da doka ta tanaza kuma ya bukaci kowa ya kwantar da hankalinsa. Ya jaddada cewa zaben ba sahihi bane.
A wani labarin kuma Gwamna Aminu Bello Masari ya taya Bola Tinubu murnan zama zababben shugaban ƙasa a Najeriya
Gwamnan Katsina ya bayyana zaben Tinubu ya zama magajin Buhari da abu mai kyau da ya dace da Najeriya a yanzu.
Haka nan Masari ya ƙara rokon mazauna jihar Katsina su fito ranar 11 ga watan Maris, su zabi Dakta Dikko Umaru Radda, ya gaje shi.
Asali: Legit.ng