Tsohon Gwamnan Katsina Ya Nemi Atiku Da Ya Amshi Sakamakon Zaɓe

Tsohon Gwamnan Katsina Ya Nemi Atiku Da Ya Amshi Sakamakon Zaɓe

  • Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema, ya nemi ƴan takara da su kai zuciyoyin su nesa sun amshi sakamakon zaɓen
  • Tsohon gwamnan wanda yana daga cikin na sahun gaba cikin magoya bayan Atiku, ya buƙace shi da ya amshi sakamakon zaɓen
  • Ibrahim Shehu Shema ya kuma shawarci hukumar zaɓe da ta toshe kunnuwanta kan kalaman da ake kanta marasa daɗi

Katsina- Tsohon gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema, wanda ɗan mutun Atiku Abubakar ne, ya roƙi dukkanin ƴan takarar zaɓen shugaban ƙasa, da su yi na'am da sakamakon zaɓen domin samun zaman lafiya da haɗin kai a ƙasa.

A dalilin hakan, tsohon gwamnan na jihar Katsina ya nemi dukkanin ƴan takarar da suka fafata a zaɓen da su yi magana da murya ɗaya domin samun zaman lafiya, haɗin kai da daidaito a ƙasar. Rahoton Vanguard

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Wasu Abubuwa 5 Da Suka Taimaka Wajen Samun Rashin Nasarar Rabiu Kwankwaso

Shema
Tsohon Gwamnan Katsina Ya Nemi Atiku Da Ya Amshi Sakamakon Zaɓe Hoto: 9news
Asali: UGC

Ibrahim Shema ya kuma yi nuni da cewa duk duniya babu inda ake samun zaɓen da ba za ayi korafi akan sa ba.

Shema ya kuma yi kira ga ƴan siyasa, malaman addini, sarakuna da ƴan kasuwa da su haɗa kan su wajen ƙara rainon jaririyar dimokuraɗiyyar ƙasar nan.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sai dai, Shema yayi ga hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) da ta duba ƙorafe-ƙorafen da akayi akan zaɓen, inda ya nemi hukumar da tayi hakan bisa yadda doka ta tanada. Rahoton Premium Times

Sannan kuma ya nemi hukumar zaɓen da tayi kunnen uwar shegu da zarge-zarge da zage-zagen da ake mata yayin da take sauke nauyin da aka ɗora mata.

Shema ya kuma janyo hankalin jami'an tsaro da su ƙara zage damtse wajen yin aikin dake kan su na kare rai da dukiyar ƴan Najeriya a duk inda suke.

Kara karanta wannan

Zaɓen 2023: Ƴan Daba Sun Tarwatsa Jami'an INEC Sun Hana a Bayyana Sakamakon Zaɓe

Atiku Ka Yarda Ka Faɗi Zaɓe, Kai Kuma Ayu Ka Sauka Daga Shugabancin PDP Inji Fayose

A wani labarin na daban kuma, Ayodele Fayose ya nemi Atiku da ya yarda yasha kaye a zaɓen shugaban ƙasa da aka kammala.

Fayose ya kuma buƙaci shugabam jam'iyyar PDP da yayi murabus daga muƙamin sa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng