“Idan Da Rai Da Rabo”: Fayose Ya Bukaci Atiku Ya Sake Gwada Sa’arsa a Gaba, Ya Taya Tinubu Murna

“Idan Da Rai Da Rabo”: Fayose Ya Bukaci Atiku Ya Sake Gwada Sa’arsa a Gaba, Ya Taya Tinubu Murna

  • Ayodele Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaben shugaban kasa da ya yi
  • Fayose ya bukaci Atiku da sauran yan takara da su rungumi sakamakon a yadda ya zo sannan su sake gwada sa'arsu a gaba
  • Jigon na PDP ya kuma bukaci shugaban jam'iyyarsu na kasa, Ayu Iyorchia da ya yi murabus don ciyar da jam'iyyar gaba

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose ya taya zababben shugaban kasar Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu murnar nasara da ya yi a zaben shugaban kasa da aka rantsar.

A safiyar ranar Laraba, 1 ga watan Maris nehukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar.

Zababben shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu a tsaye gaban lasifika
“Idan Da Rai Da Rabo”: Fayose Ya Bukaci Atiku Ya Sake Gwada Sa’arsa a Gaba, Ya Taya Tinubu Murna Hoto: @officialABAT
Asali: Twitter

Kamar yadda Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana cewa za a baiwa Tinubu da abokin takararsa, Kashim Shettima satifiket din cin zabe a yau da misalin karfe 3:00 na rana.

Kara karanta wannan

Na Hannun Dama Ya Ba Tinubu Shawara Ya Jawo Kwankwaso da Peter Obi a Gwamnati

Da yake martani ga nasarar da ya samu a wata wallafa da ya yi a shafinsa na Twitter a safiyar ranar Laraba, Fayose ya taya Tinubu murna.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ku karbi sakamakon zaben don ta'ayin kasa, Fayose ga Atiku da sauran yan takara

Fayose ya kuma bukaci dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, da sake gwada sa'arsa a gaba.

Tsohon gwamnan wanda ya kasance dan PDP, ya kuma bukaci shugaban jam'iyyar adawar, Iyorchia Ayu da ya yi murabus don ciyar da jam'iyyar gaba.

Ya rubuta a shafinsa:

"Ina taya Asiwaju Bola Tinubu murnar zabansa da aka yi a matsayin shugaban Najeriya na gaba. Yayin da zaben shugaban kasar ya zo karshe, ina mai umurtan sauran yan takara, musamman Atiku Abubakar da su karbi sakamakon zaben don ra'ayin kasarmu baki daya. Akwai gaba.

Kara karanta wannan

Ku rungumi kaddara: Tinubu ya tura sako mai daukar hankali ga Atiku da Peter Obi

"A bangaren shugaban PDP na kasa kuma, Iyorchia Ayu, ina kira ga ya gaggauta yin murabus saboda gazawarsa wajen ciyar da jam'iyyar gaba."

Ga wallafar tasa a kasa:

Jama'a sun yi martani

@tmscool ya yi martani:

"Wannan irin cin mutunci haka ga Atiku."

@Ebuka_Akure

"Baba je ga huta mana...Mun ji...Za mu hadu a kotu nan ba da jimawa ba."

@AbdulraufKhamiz

"Ni ba masoyin Atiku bane amma ganin bidiyon Atiku yana kuka ya karya mun zuciya …akwai taba zuciya sosai."

A baya mun ji cewa Farfesa Mahmood Yakubu, shugaban INEC na kasa ya ce ba zai sauka daga kujerarsa ba kamar yadda Atiku Abubakar da Peter Obi suka bukata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng