2023: "Rayuwa Ta Na Cikin Hatsari", Baturen Zabe Na Jihar Rivers Ya Dakatar Da Tattara Sakamakon Zabe

2023: "Rayuwa Ta Na Cikin Hatsari", Baturen Zabe Na Jihar Rivers Ya Dakatar Da Tattara Sakamakon Zabe

  • Baturen zaben Jihar Rivers ya ce ba zai cigaba da tattara sakamakon zabe ba saboda ana masa barazanar halaka shi
  • Baturen zaben ya ce wasu masa barazana suna zargin sa da yunkurin yin magudi a sakamakon zaben shugaban kasa na jihar
  • Farfesan ya ce ba zai cigaba da karbar sakamakon ba har sai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta shiga lamarin

Jihar Rivers - Jami'in tattara sakamakon zaben shugaban kasa a Jihar Rivers, Farfesa Teddy Charles Adias, ya dakatar da tattara sakamakon zaben saboda abin da ya kira barazana ga rayuwarsa.

Kafin dakatarwar, an tattara sakamakon kananan hukumomi 21 cikin 23 da ke Jihar.

Jihar Rivers
Baturen zabe na jihar Rivers ya dakatar da tattara sakamakon zabe, ya ce ana masa barazana. Hoto: @MobilePunch
Asali: UGC

Sakamakon kananan hukumomin Obio Akpor da Degema ake jira, kuma ake tsammanin za a karbe su da safiyar nan, Daily Trust ta rahoto.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Magoya Bayan Jam'iyyar Labour Na Barazanar Kashe Ni, Baturen Zaben Jihar Rivers Ya Koka

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Adias, wanda shine shugaban jami'ar tarayya, Otuoke, da ke Jihar Bayelsa, ya bayyana talata a matsayin ranar da zai karbi kananan hukumomin da suka rage.

Amma a safiyar talatar nan, ya janye kalamansa, yana mai cewa masu yi masa barazana suna zarginsa da magudin zabe a jihar.

Ya ce ya amsa kiran waya da dama daga mutanen da bai sani ba bayan an watsa lambarsa a kafafen sada zumunta.

Farfesan ya ce ba zai cigaba da karbar sakamakon ba har sai hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta shiga lamarin.

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164