Zaben 2023: Wani Gwamnan Arewa Ya Sake Rasa Kujerar Sanata Ga Jam'iyyar PDP
- Sanata Adamu Aliero ya kada gwamna Atiku Bagudu na Jihar Kebbi don zama sanatan Kebbi ta tsakiya
- Bagudu ya sha kayi a zaben da aka gudanar cikin kananan hukumomi takwas da ke Kebbi ta tsakiya
- An samu tsaiko wajen tattara sakamakon zaben biyo bayan bacewar baturen zaben mazabar Mafara a cibiyar tattara sakamakon zabe
Jihar Kebbi - An bayyana Sanata Muhammad Adamu Aliero a matsayin wanda ya lashe zaben sanatan Kebbi ta tsakiya a zaben yan majalisar dattawa, Daily Trust ta rahoto.
Baturen zabe, Prof. Abbas Yusuf, ya ce sanata Aliero ya samu kuri'a 126,588 inda ya kada Gwamna Abukakar Atiku Bagudu a zaben yan majalisar dattawa.
Ya ce Bagudu, wanda kuma shine shugaban kungiyar gwamnoni na jam'iyyar APC ya samu kuri'a 92,389.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Bagudu ya rasa kujerar sanata
An gudanar da zaben a kananan hukumomi takwas na Gwandu, Bunza, Aliero, Maiyama, Koko-Besse, Jega, Kalgo da Birnin Kebbi wanda su ne suka tada Kebbi ta tsakiya.
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta tsayar da tattatara sakamakon zaben sanatan Kebbi ta tsakiya a ranar Lahadi biyo bayan bacewar baturen zaben mazabar Mafara, a Birnin Kebbi.
An bukaci da ya koma ya yi gyare-gyare a wasu alkaluman da ke sakamakon da ya kawo cibiyar tattara sakamakon inda aka neme shi aka rasa.
Asali: Legit.ng