Zaben 2023: Obasanjo Na Son A Yi Wa Dimokradiyya Juyin Mulki, Kwamitin Kamfen Din APC Ta Yi Martani
- Kwamitin yakin neman zabe dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ta ragargaji tsohin shugaban kasa Olusegun Obasanjo kan kira da ya yi na cewa a soke wasu zabuka a kuma sake yinsu kan zargin magudi
- Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, Dele Alake, cikin sanarwar da ya fitar ya ce Obasanjo ba shi da hujja kawai ya yi wannan maganan ne kan jita-jita da ya ke ji kuma yana son yi wa dimokradiyya juyin mulki
- Alake ya kuma ce dama Obasanjo ya riga ya zabi bangare a wannan zaben duba da cewa ya fito fili ya fada wa matasa cewa su zabi Mr Peter Obi na jam'iyyar Labour kuma ya tunatar da al'umma cewa Obasanjo ya yi zabe da ake ganin shine mafi muni a 2003 da 2007
Kwamitin yakin neman zaben dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ta soki matsayar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo wanda ya yi kira da cewa a soke zabukan da ake ikirarin an yi magudi, rahoton The Cable.
A ranar Litinin, Obasanjo ya shawarci Shugaba Muhammadu Buhari ya dauki matakin gaggawa don magance tashin hankali da ka iya tasowa bayan zargin rashin jituwa a sakamakon zaben.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ya kuma ce a wuraren da aka gano cewa an yi magudi, a soke zaben sai a sake yin wani.
Da ya ke martani kan cikin wata sanarwa, Dele Alake, kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, ya zargi tsohon shugaban kasar da 'munafunci' da 'makirci', ya kara da cewa 'abin da Obasanjo ya yi kira ne na yin juyin mulki ga demokradiyya da kundin tsarin mulki.'
Sanarwar ta ce:
"An jawo hankalin mu kan watar takarda da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya fitar inda ya ke kira da a dakatar da tsarin zabe da ke gudana da soke zabukan da aka yi kan zargi mara tushe da tuhume-tuhume daga yan siyasa wadanda suka sha kaye kuma ba su girmama demokradiyya.
"Obasanjo ya ta maimaitawa jita-jitan da ya tsinto ba tare da hujja ba cewa an lalata na'urar tantance masu zabe na BVAS kuma sakamakon zaben da aka sanar na bogi ne.
"Abin bakin ciki ne tsohon shugaban kasa wanda ya kamata ya zama dattijon kasa yayin magana yana neman kawo matsala ga tsarin demokradiyya saboda son kai, girman kai da mugunta. Bai gabatar da hujja ba kan INEC da ingancin aikin da aka yi.
"Tabbas, mun san Obasanjo ya zabi bangare a wannan zaben. A ranar 1 ga watan Janairun 2023, ya fitar da rubutu mai tsawo yana goyon bayan takarar Mr Peter Obi ya kuma yi kira ga matasa su zabe shi."
Sanarwar ta cigaba da cewa:
"Martanin mu shine tsohon shugaban kasar yana da ra'ayinsa amma sakamakon zaben zai nuna ko yana da wata kima a siyasance. Sai ga shi har a akwatin Obasanjo, Peter Obi ya sha kaye a Abeokuta, Jihar Ogun. Yanzu ya fito fili cewa zaben kawai da Obasanjo zai yarda da shi shine wanda ya samar da Obi a matsayin wanda ya yi nasara.
"Shin Obasanjo na jayayya da sakamakon zaben shugaban kasa a Legas ko Delta inda Obi ya yi nasara? Idan sakamakon Legas inda Obi ya yi nasara ingantacce ne, a kan wane dalili ya ke nuna shakku kan sakamakon wasu wurare?
"Wannan makirci ne da munafinci tsantsarta. Obasanjo na son Shugaba Muhammadu Buhari ya yi datse aikin demokradiyya da ake yi kamar yadda shi ya yi a yanayi na rashin jin kunya a zabukan 2003 da 2007 da mafi yawanci aka yi ittifaki cewa shine mafi muni a tarihin siyasar mu.
"Abin farin ciki, Shugaba Buhari mutum ne mai nagarta da bin tsarin demokradiyya. Ba zai bari Obasanjo ya yaudare shi ta yadda zai bata sunansa na mai girmama demokradiyya ba a wannan batun."
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng