Tinubu Ya Lashe Zabe a Oyo, Ogun, Ondo, Ekiti, Kwara Yayin da Ake Ci Gaba Da Tattara Sakamako a Abuja
Jami'an hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) na ci gaba da tattara sakamakon zaben shugaban kasa na 2023 a matakan tarayya da na jiha.
Ana tattara sakamakon kasa a cibiyar taro ta kasa da ke Abuja karkashin jagorancin shugaban INEC, Mahmood Yakubu.
Kwamishinonin zabe na jiha ne ke tattara sakamakon jihohinsu mabanbanta.
Ana sa ran kwamishinonin zaben su dauki sakamakon kananan hukumomi a jiharsu zuwa cibiyar tattara sakamako na kasa a Abuja don yin lissafin karshe sannan shugaban INEC ya sanar da wanda ya yi nasara.
Zaben shugaban kasa na 2023: Tattara sakamakon kasa a Abuja
Zuwa yanzu, an tattara sakamakon jihohi 10 a matakin kasa a Abuja. Sune:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Jihar Ekiti
- Jihar Kwara
- Jihar Osun
- Jihar Ondo
- Jihar Ogun
- Jihar Oyo
- Jihar Yobe
- Jihar Enugu
- Jihar Lagos
- Jihar Gombe
Daga cikin jihohi 10 da aka lissafa a sama, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya lashe jihohi biyar da suka hada da Ekiti, Kwara, Ondo, Ogun da Oyo.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) , Atiku Abubakar, ya lashe jihohi uku wato Osun, Gombe da Yobe.
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party (LP) ya lashe jihohi biyu kacal wato Enugu da Lagos
Zuwa yanzu, Tinubu ya lashe jihohi kamar haka a zaben da aka tattara:
- Jihar Ekiti
- Jihar Ondo
- Jihar Kwara
- Jihar Ogun
- Jihar Oyo
Lura: Za mu ci gaba da tattaro jerin jihohin da Tinubu ya lashe yayin da ake ci gaba da tattara sakamakon zaben.
Asali: Legit.ng