Peter Obi Ya Tumurmusa Atiku da Bola Tinubu a Sakamakom Zaben Nasarawa
- Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, ya sake lallasa Bola Tinubu da Atiku Abubakar
- Mista Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya samu kuri'u mafi rinjaye a zaben da ya gudanar ranar Asabar a Nasarawa
- Nasarawa na ɗaya daga cikin jihohin da ba'a kai sakamakon zabensu Abuja ba kawo yanzu
Nasarawa - Mai neman zama shugaban kasa a inuwar jam'iyar Labour Party (LP), Peter Obi, ya lashe kuri'u mafiya rinjaye a zaben shugaban kasa da ya gudana ranar Asabar a jihar Nasarawa.
Daily Trust ta rahoto cewa Mista Obi ya samu kuri'u 191,361 yayin da abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, ya zo na biyu da kuri'u 172,922.
Atiku Abubakar, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam'iyyar PDP ne ke biye masu baya a matsayin na uku da kuri'u 147, 093.
Farfesa Ishaya Tanko, baturen zaɓe kuma mai alhakin tattara samakon zaben shugaban ƙasa da ya gudana a jihar Nasarawa ne ya sanar da sakamakon a hukumance.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Farfesa Tanko, shugaban jami'ar Jos da ke jihar Filato, ya bayyana cewa ɗan takarar shugaban kasa na jam'iyyar NNPP ya samu kuri'u 12,715, kamar yadda This day ta ruwaito.
A cewar baturen zaɓen INEC adadin mutanen Nasarawa da suka yi rijista domin kaɗa kuri'a su ne 2,552,716 kuma mutane 540,566 suka jefa kuri'a mai inganci.
Haka zalika ya ƙara da bayanin cewa na'ura ta tantance mutane 562,464 yayin da jumullar mutane 556,937 suka tsaya suka jefa kuri'a, daga cikin aka samu lalatattu 16,371.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa INEC ta fara tattara sakamakon zaɓem shugaban kasa daga jihojin Najeriya a birnin tarayya Abuja.
Atiku ya samu nasara a jihar Yobe
A wani labarin kuma Atiku Ya Lallasa Bola Tinubu, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa a Jihar Yobe
Wazirin Adamawa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya samu nasarar lashe kuri'a mafi rinjaye a jihar Yobe da ke arewa maso gabas.
Shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ɗan asalin jihar Yobe ne amma ya gaza kawo wa Tinubu kuri'u.
Asali: Legit.ng