Yan Bindiga Sun Harbe Jami'an INEC Har Lahira, Sun Jikkata Yan Bautar Kasa a Delta
- Wasu tsagerun 'yan bindiga sun halaka jami'in hukumar zabe fa ƙasa INEC a jihar Delta a hanyar dawowa daga wurin zabe
- REC na Delta, Mista Monday Tom, ya bayyana cewa maharan sun jikkata matasa masu hidima ga ƙasa da dama
- A halin yanzu Peter Obi ke jan ragama a sakamakon kananan hukumomi 14 da kawo yanzu INEC ta sanar a Delta
Delta - Rahotanni sun bayyana cewa an harbe jami'in hukumar zaɓe ta ƙasa (INEC) har lahira kuma matasa 'yan bautar ƙasa sun ji raunuka a jihar Delta.
Kwamishinan INEC mai kula da jihar Delta, Mista Monday Tom, shi ne ya tabbatar da lamarin ga yan jarida ranar Litinin 27 ga watan Fabrairu, 2023, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Da yake jawabi jim kaɗan bayan karban sakamakon zaben shugaban kasa na karamar hukumar Ukwani, REC ɗin ya ce:
"Mun gamu da matsalolin farmaki a karamar hukumar Ukwani, inda ɗaya daga cikin mu ya rasa rayuwarsa a hanyar mu ta dawowa bayan kammala zaɓe."
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Ba zato 'yan bindiga suka buɗe wa motar Bas ɗin da suke ciki wuta kuma bisa rashin sa'a suka yi ajalin jami'in INEC, haka nan sun raunata matasa 'yan bautar kasa."
"A halin yanzun masu hidima ga kasa da lamarin ya shafa suna kwance a Asibiti ana musu magani amma muna ta kokarin lalubo yadda zamu ɗauke su zuwa Asibiti a Asaba (babban birnin jiha)."
Sakamakon zaben shugaban kasa a jihar Delta
A bangaren zaben shugaban kasa kuma, kananan hukumomi 14 waɗanda kawo yanzu INEC ta sanar da sakamakon su a hukumance, jam'iyyar Labour Party ta lashe kananan hukumomi 10.
Jam'iyyar PDP ta yi nasara a ragowar kananan hukumomi huɗu da aka bayyana a jihar Delta.
Gwamnan Delta, Ifeanyi Okowa, shi ne ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a inuwar PDP.
A wani labarin na daban kuma Mutane Sun Yi Takansu Yayin da Mayakan Boko Haram Suka Kai Hari a Jihar Borno
Rahotanni sun bayyana cewa ana shirye-shiryen fara zabe maharan suka kutsa kai garin Goza da ke karamar hukumar Goza, sun jikkata mutaɓe akalla 5.
Asali: Legit.ng