Zaben 2023: Atiku Ya Lashe Zabe a Mahaifarsa Ta Jihar Adamawa Da Tazara Sosai
- Atiku Abubakar, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP ya yi nasara a jiharsa ta Adamawa da kuri'u 417,611
- Dan takarar APC, Bola Tinubu ya tashi da kuri'u 182,881 sannan Peter Obi na Labour Party ya samu kuri'u 105,645
- Ana ci gaba da dakon isowar ragowar jihohi domin fayyace wanda ya yi nasara a zaben shugaban kasar
Adamawa - Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya lashe zabe a mahaifarsa ta jihar Adamawa.
Atiku ya lallasa babban abokin hamayyarsa, Bola Tinubu na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da Peter Obi na jam'iyyar Labour Party da tazara mai yawan gaske, Channels TV ta rahoto.
Leadership ta rahoto cewa dan takarar na PDP ya samu kuri'u 417,611 yayin da Tinubu ya samu kuri'u 182,881 sannan Obi ya samu kuri'u 105,645, Rabiu Kwankwaso na New Nigerian Peoples Party (NNPP), 8,006.
A cewar jami'in tattara sakamako na jihar, Farfesa Mohammed Mele, masu zabe 764,834 aka tantance cikin 2,186,465 da suka yi rijista.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Ga kuri'un da kowace jam'iyya ta samu:
A – 654
AA – 536
AAC – 646
ADC – 3,398
ADP – 1,906
APC – 182,881
APGA – 887
APM – 650
APP – 372
BP – 522
LP – 105,645
NNPP – 8,006
NRM – 1,563
PDP – 417,611
PRP – 701
SDP – 1,944
YPP – 958
ZLP – 2,257
Zaben 2023: Tinubu ya lashe zabe a jihar Ondo
A wani labarin, mun ji cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, Bola Tinubu ya lallasa manyan abokan adawarsa wajen lashe zaben shugaban kasa a jihar Oyo.
Tinubu ya samu kuri'u 369,924 wajen doke Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP wanda ya samu kuri'u 115,463 da kuma Peter Obi na Labour Party wanda ya tashi da kuri'u guda 47,350.
Baturen zaben shugaban kasa a jihar, Farfesa Abayomi Fashina, ne ya sanar da sakamakon zaben a hedkwatar hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, INEC, da ke jihar a daren jiya Lahadi, 26 ga watan Fabrairu.
Asali: Legit.ng