APC ta Rasa Duka Sanatocinta a Jihar Arewa, An Yi Sukuwa a Kan Jam’iyya Mai-Ci
- Sanata Umaru Tanko Al-Makura ba zai zarce a Majalisar Dattawa ba a sakamakon rashin nasararsa
- Tsohon Gwamnan na jihar Nasarawa ya sha kashi a hannun wanda jam’iyyar PDP ta tsaida a 2023
- Kujerar Shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu ta koma hannun Hon. Ahmed Wadada
Nasarawa - Tsohon Gwamna a jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura ba zai samu damar komawa majalisar dattawan Najeriya ba.
A ranar Litinin, tashar yada labarai ta AIT ta rahoto cewa Umaru Tanko Al-Makura ya sha kashi a zaben majalisar dattawa da aka gudanar.
Mohammed Ogoshi Onawo wanda ya tsaya takara a karkashin jam’iyyar hamayya ta PDP, shi ne ya doke Tanko Al-Makura na APC mai-ci.
The Nation ta kawo rahoto cewa Dr. Ahmad Ashiku a matsayinsa na malamin zabe, ya bada sanarwar cewa jam’iyyar PDP tayi nasara.
Dr. Ashiku ya ce PDP ta samu kuri’u 93, 064 a kujerar Sanatan jihar Nasarawa ta Kudu, jam’yyar APC ta zo ta biyu da kuri’a 76,813 a zaben.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Rahoton ya bayyana cewa Alhaji Mohammed Agwai na NNPP ya zo na uku da kuri’u 30640.
Leadership ta rahoto cewa a kujerar Sanatan Nasara ta yamma, ‘Dan takaran SDP, Shehu Tukur ya sha kashi a hannun Hon. Ahmed Wadada
Arch. Shehu Tukur shi ne wanda Shugaban APC, Sanata Abdullahi Adamu ya tsaida a zaben.
Farfesa Nasirudeen Baba wanda shi ne jami’in hukumar INEC a zaben, ya ce SDP ta ci kuri’u 96488, APC ta samu 47717, sai kuma PDP mai 46, 820.
Zaben Ika ta Arewa maso gabas
An ji labari Malamin zaben hukumar INEC a jihar Delta, Farfesa Abraham Georgewill Owuneri ya ki karbar sakamakon Ika ta Arewa maso gabas.
INEC ta ce mutum 30, 105 aka tantance a Ika ta Arewa maso gabas, amma kuma mutum 31, 681 suka yi zabe, hakan ya jawo alamar tambaya.
Asali: Legit.ng