Peter Obi Ya Shiga Gaban Atiku da Tinubu a Sakamakon Zabe Daga Abuja
- Kawo yanzun an bayyana sakamakon zaben shugaban kasa a yankuna 5 cikin shida dake birnin tarayya Abuja
- A halin yanzun Peter Obi na jam'iyyar Labour Party ke kan gaba da kuri'u mafi rinjaye yayin da Bola Tinubu ke mara masa baya
- FCT Abuja na da kananan hukumomi 6 kuma tuni kowa ya san makomarsa a 5 saura Abuja Municipal kaɗai ake dako
Abuja - Ɗan takarar shugaban kasa a inuwar jam'iyyar Labour Party, Peter Obi, shi ne a kan gaba da kuri'u 111,275 a sakamakon zaben shugaban kasa da aka bayyana kawo yanzu a birnin tarayya Abuja.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa Mista Obi ya shiga gaban Bola Tinubu da Atiku Abubakar bayan INEC ta ayyana sakamakon kananan hukumomi 5 daga cikin Shida.
Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC ne na biyu da biyu da kuri'u 61,306 yayin da takwaransu na PDP, Atiku Abubakar, yake biye masu a matsayin na uku da kuri'u 47,336.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa yankunan da aka bayyana sakamakonsu zuwa karfe 11:30 na hantsin ranar Litinin sun haɗa da Bwari, Gwagwalada, Kwali, Abaji da kuma Kuje.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A yanayin yadda sakamakon ya nuna jam'iyyar APC ta samu nasara a Abaji da kuri'u 10,370, yayin da PDP ta tashi da kuri'u 6,888, sannan LP ta samu 2,874.
A Kuje, Obi ne ya ja gaba da kuri'u 14,257, yayin da jam'iyyar APC ta samu kuri'u 10,648, Atiku ya take masu baya da kuri'u 10,028.
Haka zalika jam'iyyar LP ta samu gagarumar nasara ta raba ni da yaro a Bwari, inda ta lashe kuri'u 67,198 yayin APC ke da 13,156, PDP kuma ta uku da kuri'u 10,385.
A Kwali APC ce ta samu nasara da jimullar kuri'u 11,242, PDP ta zo na biyu da kuri'u 9,054, sai kuma LP da ta tashi da 7,302.
Mista Obi ya sake samun kuri'u mafi rinjaye a Gwagwalada 19,694, APC na da 15,890, sai kuma PDP ta uku da kuri'u 10,981.
Yankin da ya rage kaɗai ba'a bayyana sakamakon shi ba shi ne cikin kwaryar birnin watau Abuja Municipal (AMAC).
PDP ta ci jihar Yobe
A wani labarin kuma Atiku Ya Lallasa Bola Tinubu, Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa a Jihar Yobe
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ta tumurmusa Bola Tinubu a zaben shugaban ƙasa na jihar shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan
Atiku ya samu nasara a Yobe duk da jam'iyyar APC ce take mulki karƙashin gwamna Mai Mala Buni.
Asali: Legit.ng