Rikici A APC Yayin Da Shugaban Jam'iyya Na Kasa Adamu Ya Gaza Kawowa Wa Jam'iyyarsa Kujerar Sanata A Mazabarsa

Rikici A APC Yayin Da Shugaban Jam'iyya Na Kasa Adamu Ya Gaza Kawowa Wa Jam'iyyarsa Kujerar Sanata A Mazabarsa

Nasarawa - Jam'iyyar All Progressives Congress ta rasa kujerar ta na mazabar Nasarawa ta Yamma ga dan takarar Social Democratic Party (SDP), Ahmed Wadada, a zaben majalisa na ranar Asabar.

Shugaban jam'iyyar APC na kasa ya fito daga yankin kuma yana wakiltar jam'iyyarsa a yankin a matsayin shugaban jam'iyya, Channels TV ta rahoto.

Ba a saka sunan dan takarar jam'iyyar APC, Shehu Tukur, ba a jerin sunayen INEC na yan takarar sanatan saboda shari'a da ake yi a kotu.

Adamu ya kasa kawo wa dan takarar APC, Shehu Tukur, kuri'u domin ya maye gurbin sa a majalisar ta dattawa, rahoton Channels TV.

Abdullahi Adamu
Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu sanye da babban riga da bakar hula. Hoto: Channels TV
Asali: Facebook

Baturen INEC na jihar Nasarawa West, Farfesa Nasiruddeen Baba yayin sanar da wanda ya lashe zaben a ofishin tattara sakamakon zabe a Keffi ya ce dan takarar na SDP ya samu kuri'u 96,488 yayin da APC ta samu kuri'u 47,717, PDP ta samu 46,820 sannan jam'iyyar Labour ta samu 33,228.

Kara karanta wannan

APC ta Rasa Duka Sanatocinta a Jihar Arewa, An Yi Sukuwa a Kan Jam’iyya Mai-Ci

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Jam'iyyar ta APC kuma ta sha kaye a mazabar Keffi/Kokona/Karu ga dan takarar jam'iyyar Social Democratic Party inda Gaza Gwefwi ya yi nasarar komawa kujerar sa.

Jam'iyyar SDP ta samu kuri'u 60,265, yayin da APC ta samu kuri'u 28,417, LP ta samu kuri'u 29,655 sai ita kuma PDP ta samu kuri'u 33,180 a zaben majalisar tarayya.

Hakazalika, dan takarar jam'iyyar PDP a zaben mazabar Nasarawa North, Godiya Akwashiki ya lashe zabe kuma Abubakar Dahiru shima ya yi nasarar rike kujerarsa ta Lafiya/Obi.

Kamar yadda hukumar zaben ta ayyana, jam'iyyar SDP ta samu sanatoci biyu cikin uku sannan ta samu mambobin majalisar tarayya biyu.

Mutanen hudu da suka ci zabe a karkashin jam'iyyar SDP tsaffin yan APC ne da suka sauya sheka saboda matsaloli yayin zaben cikin gida na APC a shekarar 2022.

Abdulaziz Yar'adua, kanin tsohon shugaban kasar Najeriya ya lashe zaben sanata a Katsina

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Tinubu Ya Lashe Zabe a Jihar Oyo, Ya Doke Atiku Da Kuri’u Masu Yawan Gaske

A wani rahoton kun ji cewa Kanal Abdulaziz Yar'adua, kanin tsohon shugaban kasar Najeriya marigayi Umaru Musa Yar'adua ne aka tabbatar ya yi nasara a zaben dan majalisar dattawa na tsakiyar Katsina.

Premium Times ta rahoto cewa Abdulaziz Yar'adua wanda ake yi wa lakaci da Audu Soja ya yi nasara ne karkashin inuwar jam'iyyar APC mai mulki a Katsina.

Abdulaziz Yar'adu'a ya samu kuri'u 153,512, sannan abokin fafatawarsa Aminu Surajo na PDP ya samu kuri'u 152,140.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164