Guguwa: Jam'iyyar Labour Ta Kawo Karshen Mulkin Dan Majalisa Bayan Zango Hudu A Kaduna
- Mr Mathew Donatus Kozali, dan takarar majalisar wakilai na tarayya na Kaura a jam'iyyar Labour ya kayar da Gideon Lucas Gwani na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP
- Farfesa Elijia D Ella, baturen zabe a Kaduna ya ce Mathew ya samu kuri'u 10,508 inda ya doke abokin fafatawarsa Gideon Gwani PDP, wanda ya samu kuri'u 10,508
- Farfesa Ella ya kuma ce Farfesa Benjamin Gugong na APC, ya zo na uku da kuri'u 9,919, yayin da Simon Na'Allah NNPP ya zo na hudu da kuri'u 5,354
Kaduna - Dan takarar jam'iyyar Labour na majalisar wakilai na tarayya mai wakilatar mazabar Kaura, a jihar Kaduna, Mr Mathew Donatus Kozali ya kayar da bulaliyar majalisa na marasa rinjaye a majalisar wakilai na tarayya, Gideon Lucas Gwani.
Kamar yadda Daily Trust ya rahoto Kozali ya samu kuri'u 10,508 yayin da shi kuma Gwani ya samu kuri'u 10,297.
Da ya ke sanar da sakamakon zaben a sakateriyar karamar hukumar Kaura a kudancin Kaduna, Baturen zabe, Farfesa Elijia D Ella, ya ayyana Mr Mathew Donatus Kuzai a matsayin wanda ya lashe zaben.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Sakamakon zaben kamar yadda baturen zabe ya sanar
Ya ce Mathew ya samu kuri'u 10,508 inda ya doke abokin fafatawarsa kuma wanda ke kan kujerar, Gideon Gwani na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, wanda ya samu kuri'u 10,508.
Kamfanin Dillancin Labarai na kasa, NAN, ta rahoto cewa dan majalisar na PDP da aka kayar yana shirin komawa majalisar karo na biyar kenan.
Baturen zaben ya ce Farfesa Benjamin Gugong na jam'iyyar All Progressives Congress, APC, ya zo na uku da kuri'u 9,919, yayin da Simon Na'Allah na jam'iyyar New Nigeria Peoples Party ya zo na hudu da kuri'u 5,345.
Ya yi bayanin cewa an tantance jimillar masu zabe 36,983 cikin guda 101,624 da suka yi rajista a karamar hukumar.
Ya kara da cewa cikin mutane 36,983 da aka tantance, 36,133 sun kada kuri'unsu.
Kalamansa:
"Mr Donatus Mathew na jam'iyyar Labour, kasancewa ya cika ka'idojin da doka ta tanada na samun kuri'u mafi rinjaye, an ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben."
Shugaban majalisa Ahmada Lawan ya ce mutanen mazabarsa sun yi yanka da azumi don ya ci zabe
A wani rahoton, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya ce mutanen mazabarsa sun yanka dabobi irinsu rakuma da shanu tare da yin azumi don ganin ya samu nasara a zaben sanata na Arewacin Yobe.
Asali: Legit.ng