INEC Ta Karbi Sakamakon Kananan Hukumomi 10 Cikin 20 a Jihar Ogun
- Hukumar zabe INEC fa buɗe zauren tattara sakamakon zabe daga kananan hukumomi 20 da ke faɗin jihar Ogun
- Kwamishinan zabe na jihar (REC), Niyi Ijalaye, ya sanar da shugaban jami'ar Ibadan a matsayin baturen zaben Ogun
- Ya ce tuni masu rike da sakamakon yadda ta kaya a kananan hukumomi 10 suka kariso, kuma an fara karba daga gare su
Ogun - Hukumar zabe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta tabbatar da cewa sakamakom zaben kananan hukumomi 10 daga cikin 20 da ke jihar Ogun sun iso hannunta.
Kwamishinan zaɓe mai kula da jihar (REC), Mista Niyi Ijalaye, ne ya bayyana haka ranar Lahadi yayin buɗe zauren tattara sakamakon zaben shugaban kasa a Abeokuta, babban birnin Ogun.
Haka zalika ya sanar da shugaban jami'ar Ibadan (UNIBADAN), Farfesa Kayode Adebowale, a matsayin baturen zabe mai tattara sakamako a jihar, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
Wane kananan hukumomi ne sakamakonsu ya iso?
Mista Ijalaye ya jero sunayem kananan hukumomin da sakamakonsu ya ƙariso zauren INEC wanda suka haɗa da Remo ta arewa, Ikenne, Egbado ta kudu da kuma Ewekoro.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Sauran kuma su ne, Abeokuta ta arewa, Ijebu ta arewa, Ijebu ta arewa maso gabas, Imeko Afon, Odeda da kuma Egbado ta arewa.
Bola Tinubu ya lashe guda 10
Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar APC, ya lashe zaben kananan hukumomi 10 cikin 20 da INEC ta bayyana kawo yanzu a jihar Ogun.
Legit.ng Hausa ta tattara maku sakamakon kamar haka;
Remo Ta Arewa
APC- 5814
PDP – 3627
LP – 984
NNPP – 22
Ikenne
APC – 9431
PDP – 6616
LP – 2698
NNPP – 39
Egbado Ta Kudu
APC – 18471
PDP – 5012
LP – 3126
NNPP – 117
Ewekoro LG
APC – 9,778
PDP – 3646
LP – 2287
Abeokuta Ta Arewa
APC – 20,094
PDP – 5057
LP – 4092
Ijebu Ta Arewa LG
APC – 21,844
PDP – 7233
LP – 2372
Ijebu Ta Arewa Maso Gabas
APC – 7430
PDP – 2,859
LP – 1779
Imeko Afon
APC – 12,146
PDP – 4560
LP – 568
NNPP – 32
Odeda
APC – 12945
PDP 3855
NNPP – 73
Ijebu Ode
APC – 16072
PDP – 4057
LP – 3162
NNPP – 56
Asali: Legit.ng