Peter Obi Ya Lallasa Tinubu A Akwatin Zaben Shugaban Kamfen Dinsa
- Gwamnan jihar Plateau, Simon Lalong ya sha kaye a akwatin zabensa ya gaza samar wa mai gidansa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu nasara
- Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour shine ya yi nasarar samun kuri'u mafi rinjaye a akwatin zaben na 015, Kutumbo Ward B na karamar hukumar Shendam, Plateau
- Kamar yadda Sowon Stephen, jami'in zabe na akwatin ya sanar, ya ce Peter Obi na jam'iyyar Labour ya samu kuri'u 104, Tinubu 88 sai Atiku Abubakar na PDP ya samu 8
Jihar Plateau - Direkta Janar na kwamitin yakin neman zaben Tinubu, kuma gwamnan jihar Plateau, Simon Bako Lalong, ya gaza kawo wa mai gidansa akwatin zabensa, rahoton Daily Trust.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour, Peter Obi, shine ya yi nasara a akwati na 015, Kutumbo Ward B na karamar hukumar Shendam ta Jihar Plateau.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Lalong ya na takara kujerar sanata ta mazabar Plateau South a zaben ranar Asabar. Ya kada kuri'arsa a Unit 015 da ke makarantar firmare ta LEA a Ajikamai.
Sowon Stephen, jami'in zabe na akwatin, ya sanar cewa Peter Obi na jam'iyyar Labour, ya samu kuri'u 104, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Peoples Progressives Congress, APC, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya samu kuri'u 88, yayin da Atiku Abubakar na jam'iyyar Peoples Democratic Party ya samu kuri'u 8.
Ga sakamakon zaben a kasa:
Shugaban kasa
APC: 88
PDP: 8
LP: 104
Sanata
APC: 143
PDP: 39
LP: 14
Yan Majalisar Tarayya
APC: 133
PDP: 47
LP: 19
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng