Dino Melaye Ya Kawo Wa Atiku Akwatinsa A Kogi, Duba Sakamakon
- Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, ya kayar da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da Mr Peter Obi a jihar Kogi
- Hakan na zuwa ne a yayin da Sanata Dino Melaye ya kawo wa Peoples Democratic Party, PDP akwatin zaben yankin sa a dukkan matakai a jihar
- Dan majalisar na majalisa zubi ta 8 wanda ya kawo wa mai gidansa mazabarsa a jihar Kogi, ya yaba wa INEC kan amfani da na'urar BVAS
Jihar Kogi - Wani rahoto da jaridar Punch ta rahoto ya nuna cewa jigon jam'iyyar Peoples Democratic Party, PDP, daga jihar Kogi, Sanata Dino Melaye, ya kawo wa mai gidan sa, dan takarar shugaban kasa na PDP, Alhaji Atiku Abubakar.
Mai magana da yawun kwamitin yakin neman zabe na Atiku-Okowa ya lashe akwatin sa a Unit 004 Aiyetoro/IIuhagba mazaba ta 1.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Legit.ng ta tattaro cewa jam'iyyar ta PDP ta lashe mafi yawan kuri'u a zaben shugaban kasa, sanata da majalisar tarayya na wakilai.
Jam'iyyar ta PDP ta samu kuri'u 125 a zaben shugaban kasa, 116 a zaben kujerar sanata sai kuma kuri'u 103 a zaben yan majalisar wakilai na tarayya.
Ga cikakken sakamakon zaben a mazabar a kasa:
Mazabar Sanata Dino Melaye. UNIT 004 Aiyetoro/Iluhagba Ward 1
Shugaban kasa
PDP: 125
APC: 31
LP: 0
Sanata
PDP: 116
APC: 20
ADC: 34
LP: 0
Majalisar Wakilai na Tarayya
PDP: 103
APC: 17
ADC: 62
Peter Obi na LP ya kayar da Bola Tinubu a akwatin zaben shugaban kamfen dinsa
A wani rahoton kun ji cewa Gwamna Simon Lalong ya kasa kawo wa mai gidansa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu kuri'u mafi rinjaye a akwatinsa.
Gwamnan Jihar Filato din shine shugaban kwamitin kamfen din shugaban kasa na jam'iyyar APC a zaben shekarar 2023.
Asali: Legit.ng