Da Dumi-Dumi: Yan Daba Sun Farmaki Rumfar Zabe a Kogi, Sun Bindige Mai Jefa Kuri’a

Da Dumi-Dumi: Yan Daba Sun Farmaki Rumfar Zabe a Kogi, Sun Bindige Mai Jefa Kuri’a

  • Wasu yan bindiga da ake zaton yan dabar siyasa ne sun farmaki rumfunar zabe a yankin Kogi ta gabas da ke jihar Kogi
  • Mahara sun bindige wani matashi a wata rumfar zabe da ke yankin Anyigba da ke kamaramar hukumar Dekina
  • A halin yanzu, hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta ta soke zabe a wasu rumfuna bakwai a jihar Kogi

Kogi - Yan bindiga sun bindige wani matashi mai suna Akayama a yankin Anyigba da ke kamaramar hukumar Dekina ta jihar Kogi.

Wau yan daba da suka farmaki garin don sace kayan zabe ne suka bindige matashin har lahira, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Taswirar jihar kogi da ke arewa ta tsakiya
Da Dumi-Dumi: Yan Daba Sun Farmaki Rumfar Zabe a Kogi, Sun Bindige Mai Jefa Kuri’a Hoto: Channels tv
Asali: UGC

Lamarin ya afku ne da misalin karfe 11:00 na safiyar yau Asabar, 25 ga watan Fabrairu inda ake gudanar da zaben shugaban kasa a fadin kasar.

Kara karanta wannan

Yan Sanda Sun Kama Mutum 15 a Wata Jihar Arewa Suna Shirin Kawo Tsaiko Ga Sakamakon Zabe

Yan daban sun mamaye garin suna ta harbi kan mai uwa da wahabi sannan suka dungi sace kayan zabe daga mazabu daban-daban.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An harbe maarigayin wanda mazauna yankin suka yi ikirarin cewa ya kammala karatunsa a bangaren ilimin tattalin arziki a jami'ar Prince Abubakar Audu, Anyigba, a wata rumfar zabe da ke in Iji-Anyigba.

Lamarin ya hargitsa zaben da ke gudana a garuruwan Dekina, Agbeji, Ajiolo, Abejukolo da Ejule yayin da yan daba suka kwace rumfunar zabe, suna kora masu zaben da basa biyayya ga wata jam'iyya.

A halin yanzu, an ce an tura sojoji domin su dawo da zaman lafiya a yankin.

INEC ta soke zabe a rumfunar zabe 7 a yankin Kogi ta gabas

A halin da ake ciki, jaridar Vanguard ta rahoto cewa an soke tsarin zabe a rumfunar zabe bakwai a yankin Kogi ta gabas.

Kara karanta wannan

Karin bayani: Bayan halartar taro kan zaben gobe, shugabar karamar hukuma ta kwanta dama

Yayin da aka soke zabe a rumfunar zabe biyu a Anyigba, karamar hukumar Dekina, sauran rumfuna biyar da aka soke zaben sun kasance a yankin Omala ta jihar Kogi.

Daya daga cikin rumfar da aka soke ita ce rumfar 01, gudunmar Abejukoli da ke karamar hukumar Omala.

Shugaban PDP na Abuja ya mutu a ranar zabe

A wani labari na daban, mun ji cewa shugaban jam'iyyar PDP na Abuja ya gamu da ajalinsa sakamakon hatsarin mota da ya ritsa da shi a ranar zabe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng