'Yan Takarar Sanata 8 Sun Janyewa Ɗan Takarar APC a Jihar Niger

'Yan Takarar Sanata 8 Sun Janyewa Ɗan Takarar APC a Jihar Niger

  • Ana gobe zaɓe, ɗan takarar sanatan jam'iyyar APC ya samu wani gagarumin tagomashi
  • Ƴan takara takwas na jam'iyyun adawa sun ce sun janye sun haƙura da yin takara inda suka mara masa baya
  • Ƴan takarar sun bayyana dalilan da ya sanya suka haƙura da takarar su domin marawa sanatan baya

Niger- Ɗan takarar sanatan Niger ta Yamma a ƙarƙashin jam'iyyar All ProgressivesɓCongress (APC), Sanata Muhammad Sani Musa, ya samu wani babban tagomashi ana gobe zaɓe.

Ƴan takara takwas ne na jam'iyyun adawa suka janyewa ɗan takarar na jam'iyyar APC a zaɓen da za a gudanar gobe. Rahoton Tribune

Jam'iyyar APC
'Yan Takarar Sanata 8 Sun Janyewa Ɗan Takarar APC a Jihar Niger Hoto: Twitter/APCNigeria
Asali: UGC

Ƴan takarar waɗanda suka kafa ƙungiyar G8, sun bayyana cewa sai da suka yi tankaɗe da rairaya na dukkanin ƴan takarar dake neman kujerar sanatan kafin su yanke shawarar marawa sanata Muhammad Sani Musa baya.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari Yayi Allah Wadai Da Kisan Ɗan Takara Ana Dab Da Zaɓe, Ya Ba Jami'an Tsaro Wani Umurni

Kakakin ƙungiyar ta su kuma ɗan takarar jam'iyyar ADC, Alhaji Usman Babagiwa, yace sanatan shine wanda ya cancanci da ya cigaba da riƙe kujerar duba da nasarorin da ya samu. Rahoton New Telegraph

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Sun bayyana dalilan su

”Mun fahimci cewa ɗan takarar APC ya samu nasarori sosai a cikin shekaru huɗun da yayi akan mulki, musamman a wajen samarwa mata da matasa ayyukan yi." A cewar sa. 
Ya bayyana cewa sun yanke shawarar haƙura da takarar su domin goyawa ɗan takarar APC baya saboda yana da ƙoƙarin samo ayyukan cigaba ga mazaɓar da jihar gabaɗaga.
”Muna da masaniyar cewa, idan aka bashi damar komawa karo na biyu, zai yi abinda yafi wanda yayi a karon farko, duba da yadda ya nuna jajircewar sa."

Ƴan takarar sanatan da suka marawa ɗan takarar APC baya sune Alhaji Usman Babagiwa na jam'iyyar ADC, Yakubu Aliyu Ibrahim na jam'iyyar SDP, Mohammed  Mohammed na jam'iyyar NRM.

Kara karanta wannan

Hasashen Zaɓen 2023: Jerin Jihohin Da Kowanne Daga Cikin Manyan Ƴan Takara 4 Zai Lashe Babu Tantama

Sauran sun haɗa da Ibrahim Bagudu  Adamu na jam'iyyar Labour Party, Mohammed Adamu na jam'iyyar APGA, Bawa Danlami na jam'iyyar APP,  Aminu  Halidu na jam'iyyar Accord da Mohammed  Bawa Ayishi na jam'iyyar ADP.

A wani labarin na daban kuma hukumar EFCC ta cafke kuɗin siyan ƙuri'a a jihar Legas.

Kamun na zuwe ana gobe babban zaɓen Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng