Zabe Ya Gabato, Har Yanzu Babban Ministan Buhari Ya Ki Yarda Ya Goyi Bayan Tinubu

Zabe Ya Gabato, Har Yanzu Babban Ministan Buhari Ya Ki Yarda Ya Goyi Bayan Tinubu

  • Sanata Chris Ngige ya sake jaddada cewa bai da wani ‘dan takara a zaben shugabancin Najeriya
  • Ministan kwadago da samar da ayyuka na tarayya ya karyata rade-radin cewa yana kushe Peter Obi
  • Ngige bai da ‘dan takara tsakanin Atiku Abubakar, Bola Tinubu, Rabiu Kwankwaso da kuma Obi

Abuja - Ministan kwadago da samar da ayyukan yi na kasa, Chris Ngige ya nesanta kansa daga jita-jitar goyon bayan wani ‘dan takara a zaben 2023.

Sun ta rahoto Sanata Chris Ngige ya fitar da jawabi ranar Laraba a garin Abuja, ya na karyata wannan labari da yake yawo a shafukan sada zumunta.

A jawabin, Ministan ya ce wasu miyagun mutane ne suka kitsa labarin bogi kuma ake ta yadawa saboda neman abin Duniya daga wajen iyayen gidansu.

Tsohon Gwamnan na Anambra ya yi kira ga daukacin jama’a su yi watsi da rade-radin da ke yawo.

Kara karanta wannan

Shugaban Kasa: Karfi da Raunin Tinubu, Atiku, Obi, Kwankwaso a Zaben Ranar Asabar

Ngige yana kashewa Obi kasuwa?

Sanata Ngige ya karyata cewa ya fadawa mutanen kasar Ibo su guji zaben Peter Obi domin za su yi asarar kuri’arsu ne kurum a jam’iyyar adawa ta LP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Haka zalika jawabin Ministan ya karyata batun cewa ya fito yana kiran ‘yan takaran LP da PDP da barayi da suke neman mulki domin su gallazawa jama’a.

Tinubu
Taron Kamfen APC Hoto: @officialasiwajubat
Asali: Facebook

Vanguard ta ce Ngige ya jaddada matsayarsa na kin goyon bayan Bola Tinubu ko waninsa, ya ce duka manyan 'yan takaran na 2023, abokan siyasar ne.

"Labarin ya kara da na cika-baki cewa ‘yan APC za su cigaba da mulki a 2023, kuma Asiwaju Ahmed Bola Tinubu zai gaji Muhammadu Buhari.
Gaskiya ban cika maida martani a kan duk abin da na gani a dandalin sada zumunta ba domin na san yadda ake yaudarar da-daman mutane a cikinsu.

Kara karanta wannan

Canza Kudi: Gwamnatin Buhari ta Fadi Irin Hukuncin da ke Jiran ‘Ganduje da El-Rufai’

Amma ganin yadda ‘yanuwa da abokai da jama’a suka taso waya ta a gaba da kira, dole in yi amfani da wannan dama domin in karyata rahoton."

- Chris Ngige

Minista ya soki Jigon APC

Rahoton ya ce Ministan kwadagon ya caccaki Josef Onoh a dalilin jero sunansa a cikin ‘yan siyasar da suka amfana da APC, amma ba su taimaki kowa ba.

Ngige ya ce ba zai iya kula Onoh wanda shi ne Kakakin kwamitin yakin neman zaben APC a Kudu maso gabas ba, sai dai mahaifinsa watau Cif C.C. Onoh.

A cewar Ministan idan manya suka hango abu, ko da yaro yana kan bishiyar kwakwa ba zai gani ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng