Shugabannin Jam'iyyar Peter Obi Sun Ce Zai Sha Kashi a Zaɓen Shugaban Ƙasa

Shugabannin Jam'iyyar Peter Obi Sun Ce Zai Sha Kashi a Zaɓen Shugaban Ƙasa

  • Shugabannin jam'iyyar Labour Party (LP) na jihohi sun kwarewa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar zani a kasuwa
  • Shugabannin sun nuna takaicin su kan yadda ɗan takarar ya mayar da su saniyar ware a jam'iyyar
  • Sun kuma bayyana cewa nasara tayi hannun riga da ɗan takarar shugaban ƙasar a zaɓen ranar Asabar

Shugabannin jam'iyyar Labour Party (LP) na jihohi 36 a Najeriya, sun bayyana cewa ɗan takarar jam'iyyar a zaɓen shugaban ƙasa ba zai iya yin nasara ba a zaɓen na ranar Asabar.

Hakan a cewar su zai faru ne saboda yayi watsi da shugabanni 36 na jihohin a yayin da yake yaƙin neman zaɓen sa da neman ƙuri'u. Rahoton The Nation

Peter Obi
Shugabannin Jam'iyyar Peter Obi Sun Ce Zai Sha Kashi a Zaɓen Shugaban Ƙasa Hoto: The Nation
Asali: UGC

Shugabannin sun bayyana cewa Peter Obi, bai basu wani muhimmanci ba inda ya zaɓi yayi aiki da wasu daban ba su ba.

Kara karanta wannan

Hasashen Zaɓen 2023: Jerin Jihohin Da Kowanne Daga Cikin Manyan Ƴan Takara 4 Zai Lashe Babu Tantama

Shugaban jam'iyyar na jihar Gombe kuma kodinetan shugabannin jam'iyyar na jihohi, Sani Abdulsalam, shine ya bayyanawa ƴan jarida hakan a birnin tarayya Abuja. Rahoton PM News

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Shugaban yace wannan halayyar da Peter Obi ya nuna zata kawo wa jam'iyyar babban naƙasu a zaɓen shugaban ƙasar.

Sun bayyana dalilan su

A kalamansa:

“Ina magana a madadain shugabanni 36 na jihohi a matsayina na kodineta."
“Shugabannin jam'iyyar basu taɓa ganin mutuncin mu ba sannan ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar mu baya ganin mutuncin shugabannin jam'iyya na jihohi."
Har ya zuwa yanzu, ba a turawa shugabannin jihohi ko asi ba, sannan bayanin da muke samu ya tabbatar da cewa an bayar da kuɗin ne ta hanyar yin la'akari da ƙabilanci da addini, saboda wasu tsirarun mutane ne kawai na wata ƙabila
suke jan ragamar yaƙin neman Peter Obi tare da haɗin bakin shugaban jam'iyya na ƙasa, waɗanda suka haɗu suka gurɓata mana jam'iyya.

Kara karanta wannan

Saura Kwana Biyu Zaɓe, Tinubu Yayi Wani Babban Kamu A Abuja

Hakan ya sanya a matsayin mu na mambobin kwamitin gudanarwa na jam'iyyar nan, muka yanke cewa Peter Obi, ba zai yi nasara ba a zaɓen nan saboda ya mayar damu saniyar ware. Bai shirya yin takarar shugaban ƙasa yadda yakamata ba.

A wani labarin kuma, hukumar INEC ta fitar da wata muhmiyar doka ana dab da a fara zaɓe a Najeriya

A ranar Asabar 25 ga watan Fabrairun 2023, za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ƴan majalisun tarayya a faɗin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng