An Shiga Zullumi A Jam'iyyar LP Yayin Da Dan Takarar Gwamna A Jihar Arewa Ya Yi Watsi Da Obi Ya Rungumi Tinubu

An Shiga Zullumi A Jam'iyyar LP Yayin Da Dan Takarar Gwamna A Jihar Arewa Ya Yi Watsi Da Obi Ya Rungumi Tinubu

  • Dan takarar gwamna na jam'iyyar Labour a jihar Adamawa, Dr Umar Mustapha Muqaddas ya koma All Progressives Congress, APC
  • Muqaddas ya sanar da hakan ne a ranar Alhamis yayin wata gajeruwar taron manema labarai da ya kira a Yola, babban birnin jihar Adamawa
  • A cewar Dr Muqaddas, tsarin da jam'iyyar na LP ke kai bai dace da niyyarsa na kawo canji ba a kasa kuma an mayar da shi saniyar ware

Jihar Adamawa - Dr Umar Mustapha Muqaddas, dan takarar gwamna na jam'iyyar Labour a jihar Adamawa, ya sauya sheka zuwa jam'iyyar All Progressives Congress, APC.

Muqaddas, wanda ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar yayin taron manema labarai a Yola, babban birnin jihar, a ranar Alhamis, ya fada wa magoya bayansa su zabi APC a ranar Asabar.

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Kwana 2 Kafin Zabe, ZLP, APM, Da Wasu Jam’iyyu 8 Sun Marawa Tinubu Baya

LP a Jihar Adamawa
Dan takarar gwamna na LP a Adamawa yayin jawabinsa na komawa APC. Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Asiwaju Bola Tinubu shine dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC, yayin da Peter Obi shine dan takarar tsohuwar jam'iyyar Muqaddas.

Muqaddas ya ce ya tattara dukkanin ofisoshinsa da jami'ansa na jam'iyyar Labour a Adamawa ya koma da su sabuwar jam'iyyarsa, Daily Trust ta rahoto.

Ya ce magoya bayansa sun shigo jam’iyyar LP ne da imanin cewa za ta samar da siyasar Najeriya cigaba ke bukata ta gaskiya, hada kai da hangen nesa.

Ya lura cewa shi da magoya bayansa sun yi takaici saboda sun tarar mutanen da ke tafiyar da jam’iyyar LP na kan mummunan tsarin da suka kokarin canzawa.

Muqaddas ya bayyana daliinsa na fita daga jam'iyya Labour

Ya koka cewa duk da kokarinsu da niyya mai kyau, sun gano cewa ba za su iya zuwa ko ina ba a jiha da kasa baki daya da irin tsarin da kwamitin kamfen din takarar shugaban kasa na Peter Obi ta shirya.

Kara karanta wannan

"Ka Janye Wa Kwankwaso", Wasu Kungiyoyi Suka Roki Atiku Kwanaki Kadan Kafin Zabe

Ya ce:

"LP ta manta da ni, an mayar da ni saniyar ware da gangan a matakin jiha da lasa, haka su ma sauran yan takarar na LP."

Dakaci karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164