“Ya Zama Dole Yan Najeriya Su Zabi Tinubu”: Inji ZLP, APM, Da Wasu Jam’iyyu 8
- Lamuran zaben 2023 na kara daukar sabon salo yayin da ake saura kwanaki biyu zaben shugaban kasa
- Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na APC, ya samu gagarumin goyon baya daga jam'iyyun adawa
- Jam'iyyun ZLP, NRM, APP, APM da wasu takwas sun ayyana goyon bayansu ga Tinubu a jihar Legas ana saura kwanaki biyu zabe
Lagos - Kudirin dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Asiwaju Bola Tinubu, ya samu gagarumin goyon baya ana gab da babban zaben kasar.
A ranar Alhamis, 23 ga watan Fabrairu, jam'iyyun siyasa 10 da yan takararsu sun ayyana goyon bayansu ga tsohon gwamnan na jihar Lagas.
Legit.ng ta rahoto cewa jam'iyyun siyasar da suka hada da ZLP, NRM, APP, APM da saurtansu sun bayyana goyon bayansu ne a wani taro da ya gudana a Asibitin Filin jirgin sama, Ikeja, Legas.
Da take magana a madadin shugabannin kowace jam'iyyar siyasa, shugaban NRM a Legas, Temilola Akinade, ta ce jam'iyyun siyasar sun lamuncewa dan takarar shugaban kasar na APC saboda shi ya fi cancanta cikin yan takarar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
ta ce:
"A madadin sauran jam'iyyun siyasa da ke nan a yau, mun goyi bayan takarar Asiwaju Bola Tinubu da dan takarar mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima.
"Mu jam'iyyun siyasa masu rijista mun yanke shawarar goyon bayan Sanata Bola Tinubu saboda ya yarda da tarayya ta gaskiya. Ya kasance mai wa'azin yan sandan jiha wadanda za su kawo zaman lafiya a kasar da kore rashin tsaro a kasar.
"Tinubu ya yarda da daidaito da adalci. Shi mutum ne da ya yarda da Najeriya daya. Mun sani sarai cewa idan ya zama shugaban kasar tattalin arzikin kasar zai bunkasa wanda zai kai ga ci gaban tattalin arziki."
Tinubu ya yarda da tarayya ta gaskiya
Akinade ta bayyana cewa jam'iyyun siyasar sun lamuncewa Tinubu saboda ya yarda da tarayya ta gaskiya da kuma kafa yan sandan jiha.
"Mun sani sarai cewa idan ya zama shugaban kasar nan, tattalin arziki zai bunkasa. Mun gamsu da cancantarsa don ci gaba da dorewar kasar. Ina umurtan yan Najeriya da su zabi Tinubu da Shettima don makoma mai kyau."
Da yake magana a taron goyon bayan dan takarar na APC a hukumance, shugaban ZLP a jihar Legas, Adekunle Adenipekun, ya ce goyon bayan ya zama dole don inganta Najeriya.
Asali: Legit.ng