Zaben 2023: Matakai Masu Sauki Da Za Ka Bi Don A Tantance Ka A Akwatin Zaben Ka

Zaben 2023: Matakai Masu Sauki Da Za Ka Bi Don A Tantance Ka A Akwatin Zaben Ka

  • Yayin da yan Najeriya ke cigaba da shirin babban zaben 2023, an shawarci masu zabe da bi tsarin kada kuri'a
  • An kuma umarci ma'aikatan zabe da su isa wuraren aikin su da wuri don gudanar da aikin su cikin sauri
  • Bugu da kari, yana da muhimmanci a sani cewa dole sai da katin zabe za a iya tantance mutum

Yayin da ya rage kasa da awa 48 don gudanar daben shugaban kasa da aka dade ana tsammani, masu kada kuri'a na ta tsuma don zuwa mazabarsu kada kuri'a ga dan takarar da su ke buri.

Sai dai, yana da kyau masu zabe dauke da katin zaben na dindindin su fahimci tsarin tantance su idan sun isa mazabunsu ranar zabe.

Shugaban INEC
Shugaban hukumar INEC, Farfesa Mahmood Yakubu yana jawabi. Hoto: INEC
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kara karanta wannan

Zaben 2023: An kai muhimman kayan aikin zabe shugaban kasa jihar Gombe, INEC ta magantu

Zuwa wajen kada kuri'a da wuri shine matakin farko na tantance mutum da wuri.

Tantancewar tana da muhimmanci a zaben mai zuwa duba da irin sababbin fasahar zamani da aka fito da su a zaben bana.

A wata mujallar shawarwari kan zabe, My Election Buddy na, tantance ma su zabe ya kunshi tabbatar da cewa mutum a mazabarsa yayi zai yi zabe.

Tantancewar na da muhimmanci yayin da ake shirin shiga babban zabe, yana da muhimmanci a san dalilan tantancewar guda hudu ne.

Yana da muhimmanci a san cewa ana tantancewar don hana kada kuri'a fiye da daya, wani ya kada kuri'ar wani, da kuma tabbatar da wanda ya cancanta ne kadai yayi zabe.

1. Dubawa ko sunan wanda zai yi zabe ya fito a rijistar masu kada kuri'a a mazabar.

2. Jami'in hukumar zabe zai tantance katin zabe ta hanyar daukar yatsa ko hoto.

3. Jami'in hukumar zabe zai tabbatar sunan wanda ya gabatar da katin zabe ne a jikin katin.

Kara karanta wannan

An Yi Kus-Kus Tsakanin Shugaban INEC Da Shugaba Buhari Game Da Zaben Ranar Asabar

4. Mai kada kuri'a yana akwatin da ya kamata ya kada kuri'a.

Hanyoyin da za abi don tantancewa

1. Ranar zabe, ka tabbatar ka isa mazaba tare da katin zaben ka.

2. Idan ka isa akwatinka, jami'in INEC mai kula da akwatin zai tantance katin, ta hanyar amfani da shatin yatsa ko hoto, ta hanyar amfani da sabuwar na'urar BVAS.

3. Idan an tantance ka, za a baka takarda wacce za ka dangwala wa jam'iyyar da ka ke ra'ayi don kada kuri'ar ka.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164