Zaben 2023: Atiku Ya Hadu Da Cikas Yayin da Jam’iyyun Adawa 5 Suka Marawa Tinubu Baya a Oyo
- Yan kwanaki kafin zaben shugaban kasa, jam'iyyun adawa biyar sun ayyana goyon bayansu ga Bola Tinubu
- Jam'iyyun adawar sun jaddada cewa APC za su yi a zaben shugaban kasa na ranar 25 ga watan Fabrairu
- Sun ce tsohon gwamnan na jihar Lagas yana da abun da ake bukata wajen gyara Najeriya da tattalin arzikinta
Oyo - Jam'iyyun siyasa biyar a jihar Oyo sun nuna goyon bayansu ga dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, a babban zaben ranar Asabar.
Jerin sunayen jam'iyyun da ke goyon bayan Tinubu
Jam'iyyun sune; Action Alliance; African Action Congress; Action Peoples Party da Booth Party, jaridar Punch ta rahoto.
Yan takarar gwamna na jam'iyyun ne suka zartar da wannan hukunci ne a wani taron manema labarai a Ibadan, babban birnin jihar a ranar Laraba, 22 ga watan Fabrairu.
Ana Gab Da Zabe, Atiku Ya Kara Karfi a Arewa, Dan Majalisa Mai Ci Da Hadimin Gwamna Sun Fice Daga APC Zuwa PDP
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban jam'iyyar Young Peoples Party a jihar, Adedeji Adeyemi, wanda ya zanta da manema labarai a wayar tarho ya samu wakilcin mataimakinsa, Adesola Adedeji a taron.
Dan takarar gwamnan jam'iyyar AAC, Okedara ya ce:
"Zan bayar da goyon bayana ga Tinubu kuma na umurci mutanena, magoya bayanmu da su zabi Tinubu a ranar Asabar saboda yana dauke da manufofinmu ta bangaren ababen more rayuwa, tallafawa matasa, kiwon lafiya da bayar da tsaro ga daukacin yan Najeriya.
"Shugabannin APC sun yi nazarin manufofina a yanar gizo kuma sun nuna a shirye suke su yi amfani da su bisa tsarin ajandar APC don sabonta Najeriya, don haka tikitin Tinubu da Kashim Shettima za mu zaba a ranar Asabar."
Dan takarar gwamna a jam'iyyar Booth party; Okunade ya ce mabiyansa sun umurce shi da ya goyawa Tinubu baya.
Ya ce:
"Bola Tinubu ya yi gwagwarmaya don tabbatar da dorewar damokradiyya a Najeriya kuma wannan yasa shi ne ya fi dacewa da shugabancin kasa saboda zai karfafa kundin tsarin mulkin damokradiyya da doka."
A nashi bangaren, dan takarar gwamnan APP, Ayandoye ya ce:
"Ni bayaraben asali ne kuma wannan takarar shine abun da Yarbawa ke so saboda zagayenmu ne.
"Goyon bayanmu ga Tinubu ya fi gaban jam'iyyar siyasa ba zan iya goyon bayan wani dan takara ba baya ga Tinubu saboda tarin nasarorinsa.
"Ina umurtan dubban magoya bayana da su yi Tinubu sannan su zabe shi a ranar Asabar."
Da yake magana, dan takarar gwamnan AA, Ajekiiigbe ya ce jam'iyyarsa ta yanke shawarar marawa Tinubu baya ne saboda abubuwan da ya yi a matsayin gwamnan Legas.
"Ina umurtan dukkan magoya bayana da su zabi Tinubu don ya zama zababben shugaban kasar Najeriya a ranar 25 ga watan Fabrairu."
Zaben 2023: PDP ta yi babban kamu a jihar Jigawa
A wani labarin kuma, mun ji cewa dan majalisar tarayya mai wakiltan mazabar Babura/Garki a jihar Jigawa, Hon. Musa Muhammed Adamu Fagengawo, ya sauya sheka daga APC zuwa PDP.
Asali: Legit.ng