2023: Dan Majalisa Mai Ci Da Hadimin Gwamna Badaru Sun Fice Daga APC Zuwa PDP a Jigawa
- Yan kwanaki kafin babban zaben 2023, jam'iyyar APC ta hadu da gagarumin cikas a jihar Jigawa
- Hadimin gwamnan jihar Hon. Bala Sule Kila da dan majalisa mai wakiltan mazabar Babura/Garki a jihar sun fice daga APC zuwa PDP
- A ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu ne za a yi zaben shugaban kasa da na yan majalisar tarayya
Jigawa - Mamba mai wakiltan mazabar Babura/Garki a jihar Jigawa, Hon. Musa Muhammed Adamu Fagengawo, ya fice daga jam'iyyar All Progressive Congress (APC) mai mulki.
Hakazalika hadimin Gwamna Mohammed Badaru Abubakar, Hon. Bala Sule Kila shima ya fice daga APC zuwa PDP.
Dalilin da yasa na bar APC zuwa PDP, Hon. Musa
Dan majalisar ya bayyana ficewarsa a cikin wata wasika dauke da sa hannunsa wanda ya aikewa shugaban APC a gudunmar Kore a karamar hukumar Garki da ke jihar, Nigerian Tribune ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hon. Musa ya ce ya yanke hukuncin ne bayan yawan rikice-rikicen da ke ta faru a dukkanin matakan jam'iyyar APC.
A cewarsa:
"Na rubuto wannan wasikar don sanar da cewa na yi murabus daga matsayin dan jam'iyyar All Progressive Congress (APC) daga ranar 21 ga watan Fabrairun 2023. Hakan ya zama dole saboda rikice-rikicen da ke faruwa a dukkan matakai na jam'iyyar."
Ya kara da cewar:
"A halin da ake ciki ina godiya ga jam'iyyar da ta bani damar takara a karkashin inuwarta."
Dan majalisar ya kuma sanar da sauya shekarsa zuwa jam'iyyar People Democratic Party (PDP).
Da yake jawabi ga manema labarai jim kadan bayan samun tarba daga dan takarar gamnan PDP a Dutse, ya ce ya yanke hukuncin ne bayan tattaunawa da mazabarsa kan shirin barin APC zuwa PDP.
Ya kuma bayyana cewa ya shiga tawagar dan takarar gwamnan PDP, Mustapha Sule Lamido, don tabbatar da nasarar jam'iyyar a zaben 2023, rahoton Daily Post.
Ya ci gaba da cewa:
"Na kasance a nan saboda ina so na taimaki abokina, mun halarci jami'a daya, na zo nan ne don taimakon jam'iyyar don ta lashe zabe."
Yan kwanaki kafin zabe, babban faston Najeriya ya fadi wanda zai ci zabe
A wani labarin, shugaban cocin Jehovah Power Miracle Tabernacle da ke Ibadan, Prophet Mike Agboola, ya yi ikirarin cewa dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar ne zai lashe zabe.
Faston ya ce Allah ya nuna masa Bola Tinubu na APC da Atiku suna kan doki kafin wani abu ya tura dan takarar na PDP gaba har ya lashe zabe.
Asali: Legit.ng