Kai Tsaye: Yadda Gangamin Kamfen Din Tinubu/Shettima Ke Gudana A Lagas

Kai Tsaye: Yadda Gangamin Kamfen Din Tinubu/Shettima Ke Gudana A Lagas

A yau Talata, 21 ga watan Fabrairu ne Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar All Progressives Congress (APC), zai gudanar da gangamin kamfen dinsa na karshe a filin wasa na Teslim Balogun Stadium (TBS) da ke jihar Lagas.

Tun bayan da ya lashe tikitin takarar shugaban kasa na APC, Tinubu ya gudanar da gangamin kamfen guda biyu a jihar da ya mulka a matsayin gwamna.

Gangamin kamfen din Tinubu a Lagas
Kai Tsaye: Yadda Gangamin Kamfen Din Tinubu/Shettima Ke Gudana A Lagas
Asali: Original

Ana sanya ran Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai jagoranci dukkanin gwamnonin jam'iyyar mai mulki da sauran masu ruwa da tsaki zuwa TBS gabannin babban zaben na ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu.

Wasu masu lura da harkokin siyasa suna ganin cewa wannan gangamin na da matukar muhimmanci ga Tinubu saboda dole ya dakushe manyan abokan hamayyarsa, Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party wadanda suka gudanar da manyan gangami a Lagas.

Zan yi wa Najeriya aiki tukuru kamar yadda Buhari ya yi mani, Tinubu a gangamin kamfen dinsa na karshe

An yi wa Asiwaju Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC kara sosai a wajen gangamin kamfen dinsa na karshe wanda ya gudana a Lagas.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya halarci gangamin ya sake daga hannun Tinubu a matsayin shugaban kasar gobe da izinin Allah.

Kamfen din Tinubu
Kai Tsaye: Yadda Gangamin Kamfen Din Tinubu/Shettima Ke Gudana A Lagas
Asali: Original

Da yake jawabi a wajen kamfen din, Tinubu wanda ke fuskantar shugaban kasar ya ce:

"Kamar yadda ka yi mun aiki tukuru, zan yi wa Najeriya aiki tukuru. Za mu bi duk wasu tsare-tsare da muka tanada a manufofinmu don sabonta muradan yan Najeriya."

Tinubu ya yi godiya ga shugaba Buhari kan tsayin daka da ya yi wajen tabbatar da damokradiyya, gaskiya da kuma adalci.

"Shugaban kasar ya bukaci dukkaninmu da muke da ra'ayi mu je mu yi takara a zaben fidda gwanin jam'iyyarmu inda daleget suka zabe ni, bai bukaci su sauya sakamakon zaben ba sanoda kabila ko addini ko saboda ni ba dan Daura bane kamar shi, ya amince da ni sannan ya tayani murna, yana mai cewa mun 'ka kusa kaiwa wajen'."

Dan takarar na APC ya ce ya zabi Sanata Kashim Shettima wanda ya bayyana a matsayin mai ilimi da sanin ya kamata a matsayin abokin takararsa.

Ya ce Shettima ya nuna jajircewa wajen gudanar da ayyukansa kuma ya bambanta, yana mai bayyana shi a matsayin mutum abun dogaro, mai amana kuma jajirtacce.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu ya yi godiya ga mutanen jihar kan yadda suka fito kwansu da kwarkwatansu don tarban shugaban kasa Buhari da Asiwaju Tinubu sannan suka kuma halarci gangamin kamfen din.

Ya ce wannan fitowar da jama’a suka yi ya nuna soyayyar da suke yiwa dan birnin, inda ya bukace su da su fito a ranar Asabar, 25 ga watan Fabrairu domin zabar Asiwaju a matsayin shugaban kasa.

Wadanda suka yi jawabi a gangamin sun hada da shugaban APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, Darakta Janar na kwamitin yakin neman zaben Tinubu Shettima kuma gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da uwargidar dan takarar shugaban kasar na APC, Sanata Oluremi Tinubu.

Ba na adawa da takarar Tinubu, ina tare da shi dari bisa dari, Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jaddada goyon bayansa ga Tinubu a zaben shugaban kasa.

Buhari ya ce baya adawa da dan takarar na APC kuma yana tare da shi dari bisa dari.

Ya kuma ce shine zai lashe zaben ranar 25 ga watan Fabrairu inda ya ce daga ranar Litinin zai koma shugaban kasa mai jiran gado.

"Ba na adawa da Asiwaju Tinubu ni nashi ne dari bisa dari…Zuwa Litinin za a kira shi da zababen shugaban kasa mai jiran gado na tarayyar Najeriya.”

Matar Tinubu, Oluremi, ta yi masa kamfen

Uwargidar Tinubu, Sanata Oluremi, ta bayyana cewa mijinta na takarar shugaban kasa ne saboda ya hango haske tattare da makomar Najeriya.

Ta ce:

"Muna a mataki mai matukar muhimmanci bayan yawon kamfen. Wannan shinbe gangamin yakin neman zabe na karshe. Asiwaju na takara ne saboda ya hango makoma mai kyau a Najeriya ga manyan gobe."

Kamfen din Tinubu
Kai Tsaye: Yadda Gangamin Kamfen Din Tinubu/Shettima Ke Gudana A Lagas
Asali: Original

Kamfen din Tinubu na Legas: Sanwo-Olu ya yi godiya ga Buhari kan halartan tarfon da ya yi

Gwamna Sanwo-Olu ya jinjinawa Buhari kan halartan gangamin kamfen din APC na karshe da ya yi a jihar Legas.

Gwamnan na Legas ya ce:

“Ina so na mika godiyata gare shi kan bamu Tinubu/Shettima da ya yi.
“Muna so mu jaddada cewar Tinubu masoyin Legas da Najeriya ne.
“Asiwaju ka ga cewa Legas ta shirya maka. Za mu zabe ka kuma za ka yi nasara a ranar Asabar.”
Buhari da Sanwo-olu
Kai Tsaye: Yadda Gangamin Kamfen Din Tinubu/Shettima Ke Gudana A Lagas Hoto: @APCPresCC2022
Asali: Twitter

Gangamin kamfen din Tinubu: Shugaba Buhari ya isa TBS

Domin nuna cikakken goyon bayansa ga kudirin takarar shugabancin Tinubu, Shugaba Buhari ya isa filin wasa na TBS don nuna goyon bayansa ga abokinsa a siyasa.

Ana ta ihun ‘Jagaban’ yayin da Tinubu, Buhari da sauran manyan jam’iyyar suka isa wajen taron.

Mazauna Legas sun kai Tinubu wajen gangamin kamfen din APC

Dubban mazauna jihar Lagas sun yi wa tsohon gwamnansu kuma dan takarar shugaban kasa APC, Bola Tinubu, rakiya har zuwa wajen gangamin kamfen din jam’iyyar da ke gudana a TBS.

Tare da shi akwai mataimakinsa, Kashim Shettima, shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan da kuma kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Tinubu
Kai Tsaye: Yadda Gangamin Kamfen Din Tinubu/Shettima Ke Gudana A Lagas Hoto: @TheNationNews
Asali: Twitter

Buhari ya isa jihar Legas don yi wa Tinubu kamfen

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya isa filin wasa na kasa da ke Surulere don halartan gangamin yakin neman zaben shugaban kasa na APC.

Mai ba shugaban kasa shawara kan shafukan sadarwar zamani, Bashir Ahmad, ya saki bidiyo da ke nuna lokacin da jirgin shugaban kasar ya sauka a jihar Lagas.

Bidiyo: Yadda mutanen Lagas suka cika da farin cikin ganin Tinubu a yankin Oshodi

Mazauna yankin Oshodi da ke jihar Lagas sun cika da farin cikin ganin Tinubu yayin da yake daga masu hannu a cikin wata mota.

Jama'a sun cika da farin ciki yayin da Tinubu ya isa Lagas don kamfen dinsa

Jama'a sun cika da farin ciki yayin da dan takarar shugaban kasa na APC kuma tsohon gwamnan Lagas, Bola Tinubu, ya isa jihar don gangamin kamfen dinsa.

Tinubu ya samu kyakkyawar tarba ta musamman daga wajen jama'ar da suka taru domin jiran isowarsa wajen kamfen din da ke gudana a yau Talata.

A bidiyon da ya yadu a Twitter, an gano Tinubu yana taka rawa yayin da ake rera wakokin yabonsa.

Jama'a sun yi cikar kwari a wajen kamfen din Tinubu a Lagas

Filin wasa na Teslom Balogun ya cika ya tumbatsa yayin da magoya baya ke jiran isowar Asiwaju Bola Ahmed Tinubu don gudanar da kamfen dinsa na karshe.

Magoya Bayan APC Da Jaruman Fim Sun Fara Hallara

A halin da ake ciki, wasu daga cikin magoya bayan jam'iyyar APC mai mulki sun isa wajen gangamin kamfen din na shugaban kasa.

Manyan jaruman fina-finan kudu wato Nollywood kamar su Saheed Balogun, Foluke Daramola, da sauransu sun isa filin taron.

An Tsaurara Matakan Tsaro a Filin Taro Na TBS

An tsaurara matakan tsaro a filin wasa na TBS yayin da ake jiran isowar shugaban kasa Muhammadu Buhari da Bola Tinubu a wajen yakin neman zaben shugaban kasar na APC.

An gano jami'an tsaro tsattsaye a wurare masu muhimmanci da za su sada mutum da filin taron.

A daidai lokacin kawo wannan rahoton, ba a bari kowa ya shiga sashin da aka tanada saboda manyan baki ba, jaridar PM News ta rahoto.

Wajen kamfen
Kai Tsaye: Yadda Gangamin Kamfen Din Tinubu/Shettima Ke Gudana A Lagas Hoto: PM News
Asali: UGC

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng