Sauya Naira: Jerin Gwamnonin APC 14 Da Suka Daura Damarar Yakar Tsarin CBN
- Gwamnonin APC 14 ne suke takun saƙa da sabon tsarin CBN na sauya fasalin naira wanda ya jefa yan Najeriya cikin wahala.
- Gwamna El-Rufai na Kaduna, Sanwo Olu na Legas, Yahaya Bello na Kogi da Matawalle na Zamfara na cikin gwamnonin
- Bayan taron da suka gudanar jiya Lahadi, gwamnonin sun bayyana cewa bakin su ɗaya game da tsarin sauya kuɗin
Abuja - A bayyane take gwamnonin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya suna adawa da sabon tsarin sauya naira kuma su ne a sahun gaba wajen yaƙar tsarin da CBN ya ɓullo da shi.
Gwamnonin da suka nuna adawarsu ga tsarin a fili na cikin waɗanda suka halarci taron gaggawa da shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Adamu, ya kira ranar Lahadi, 19 ga watan Fabrairu, 2023.
Wasu bayanai da Legit.ng Hausa ta tattaro daga majiya mai ƙarfi sun haɗa jerin sunayen gwamnonin da suka halarci ganawar, waɗanda ke jan ragamar takun saƙa da CBN.
Gwamnonin sune kamar haka;
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
1. Gwamna Simon Bako Lalong na jihar Filato
2. Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa
3. Gwamna Abubakar Sani Bello na jihar Neja
4. Gwamna Malam Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna
5. Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi
6. Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya na jihar Gombe
7. Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe
8. Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara
9. Gwamna Biodun Oyebanji na jihar Ekiti.
10. Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas
11 Gwamna Atiku Bagudu na jihar Kebbi
12. Gwamna Muhammad Badaru na jihar Jigawa
13. Gwamna Aminu Bello Masari na jihar Katsina
14. Gwamna Hope Uzodinma na jihar Imo.
Wace matsaya gwamnonin APC suka cimma kan tsarin sauya naira?
Yayin ganawa da Abdullahi Adamu, gwamnonin karkashin inuwar kungiyar gwamnonin ci gaba na APC (PGF) sun bayyana a fili cewa duk bakinsu ɗaya kan batun karancin naira.
Da yake ƙarin haske kan haka, shugaban PGF, gwamna Atiku Bagudu ya ce baki ɗaya takwarorinsa sun amince da matsayar da taron ya cimmawa, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
A kalamansa, Bagudu ya ce:
"Duk bakin mu ɗaya, ƙungiyar gwamnonin ci gaba da kwamitin gudanarwa NWC duk jam'iyya ɗaya ce, dukkan mu abu ɗaya ne."
A wani labarin na daban kun ji cewa Bola Tinubu ya kutsa wurin taron shugaban APC da gwamnoni a Abuja
Sanata Abdullahi Adamu, ya gayyaci gwamnonin jam'iyyar APC zuwa zaman tattauna wa kan halin kuncin da sauya naira ya jefa 'yan Najeriya.
Taron wanda ya gudana jiya Lahadi, ya samu halartar gwamnoni sama da 10, ba zato sai ga Bola Tinubu ya shiga cikin ganawar.
Asali: Legit.ng