Canza Kudi: ‘Dan Majalisar Kaduna Ya Bukaci Cafke El-Rufai Saboda Umarnin da ya bada
- Hon. Samaila Suleiman ya ce umarnin da Malam Nasir El-Rufai ya bada tamkar cin amanar kasa ne
- ‘Dan majalisar na PDP ya fitar da jawabi, yana raddi a kan kokarin halatta tsofaffin N500 da N1000
- Abin da Suleiman yake so shi ne da zarar Gwamna Rufai ya bar mulki, jami’an tsaro su yi ram da shi
Kaduna - ‘Dan majalisar wakilan tarayya na Kaduna ta Arewa, Samaila Suleiman ya soki matsayar da Gwamna Nasir El-Rufai ya dauka a kan canjin kudi.
A rahoton da Tribune ta fitar, Honarabul Samaila Suleiman ya zargi Malam Nasir El-Rufai da cin amanar kasa da yi wa kundin tsarin mulki karon tsaye.
Ganin irin kalaman da Gwamnan yake yi wanda sun ci karo da umarnin shugaban Najeriya ‘dan majalisar ya nemi jami’an tsaro su cafke Nasir El-Rufai.
A yanzu ba za a iya kama shi ba, Sun ta ce Hon. Samaila Suleiman yana so doka tayi aiki a kan Mai girma Nasir El-Rufai ne bayan ya bar ofis a watan Mayu.
Sabawa tsarin mulkin kasa
Rahoton ya ce ‘Dan majalisar ya fitar da jawabi na musamman a ranar Lahadi, yana cewa kalaman Gwamnan kan batun canjin kudi, cin amanar kasa ne.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
‘Dan adawar yana zargin Gwamnan na jihar Kaduna da yin abin da zai zama raini ga kujerar shugaban kasa, yana halattawa jama'a tsofaffin N500 da N1000.
"A kan wannan gaba, wannan jawabi yake kira ga jami’an tsaro suyi harama, su shirya kare tsarin damukaradiyya da daraja da hadin-kan Najeriya.
A tabbata an cafke Nasir El-Rufai kuma an gurfanar da shi bisa laifin cin amanar kasa wanda babban laifi ne ga damukaradiyya da kasa baki daya."
- Hon. Samaila Suleiman
A rahoton The Guardian, Hon. Sulaiman ya ce abin mamaki ne El-Rufai zai rika irin wannan magana alhali bai kaunar talakawa ko bin umarnin kotu.
A ra’ayin Sulaiman, umarnin da Gwamna El-Rufai ya bada yana iya zuga mutanen jihar Kaduna su yi bore a kan gwamnatin da al’ummar kasa suka zaba.
A matsayinsa na ‘dan majalisa, Honarabul din ya ce ya san ba za a iya taba Gwamna a yanzu ba, sai bayan ya bar ofis daga ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Harka ta tsaya cak a yau
Wani rahoto da muka fitar, ya bayyana yadda canjin kudi ya yi wa karuwanci tasiri. Wasu mata masu zaman kansu a Abuja sun fadi wahalar da suke sha.
Saboda karancin kudi, ana samun tangarda wajen turawa ‘yan mata kudi cikin asusun bankinsu. Wata mai zaman kan ta, ta ce dole farashi ya sauka.
Asali: Legit.ng