NEF Ta Fusata Ta Nesanta Kanta Da Marawa Atiku Abubakar Baya

NEF Ta Fusata Ta Nesanta Kanta Da Marawa Atiku Abubakar Baya

  • Ƙungiyar dattawan Arewa ta nesanta kanta da marawa Atiku Abubakar baya a zaɓe mai zuwa
  • Ƙungiyar tace har yanzu bata da wani ɗan takarar shugaban ƙasa da take marawa baya a zaɓen dake tafe
  • Seidu Baba wani mamba a ƙungiyar shine ya nesanta ƙungiyar da marawa Atiku baya

Wani mamba a ƙungiyar dattawan Arewa, Seidu Baba, ya bayyana cewa har yanzu ƙungiyar bata da ɗan takarar shugaban ƙasan da take marawa baya a zaɓen dake tafe.

Da yake magana da ƴan jarida a wajen wani taron murnar cika shekara goma na ƙungiyar. Seidu Baba yayi watsi da ƙus-ƙus ɗin ake yi cewa Atiku Abubakar na jam'iyyar PDP, shine ɗan takarar ƙungiyar. Rahoton The Cable

Atiku
NEF Ta Fusata Ta Nesanta Kanta Da Marawa Atiku Abubakar Baya
Asali: UGC

Seidu ya bayyana cewa Atiku Abubakar bai yiwa yankin Arewacin Najeriya adalci ba wanda hakan ya sanya ruwa na neman ƙarewa ɗan kada.

Kara karanta wannan

Rayuwa a Hannun Ƴan Bindiga: Halin Da Ragowar Ɗaliban FGC Yauri Suke Ciki

Ba a ganin Atiku a matsayin wani wanda yake da kusanci da Arewa saboda bai yi mana adalci ba, wani mutum ne shi wanda baya zama a Arewa." A cewar sa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Baba yace yunƙurin da akayi na neman ƙungiyar dattawan Arewa ta marawa Atiku baya ya nuna yadda yake neman mulkin ido rufe.

Saidu Baba yace duk ƙoƙarin da akayi na ganin cewa ƙungiyar dattawan Arewa ta goyi bayan Atiku, ƙungiyar bata amince ta mara masa baya ba. Rahoton Daily Post

Mutane da gawa sun yi amanna cewa duk da cewa gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya caccaki dattawan Arewa, babban wanda yake hari shine Atiku Abubakar." Inji shi
“Babu yadda za ayi ace Atiku shine ɗan takarar Arewacin Najeriya saboda bai san mu ba, sannan mu ma bamu san shi ba."

Kara karanta wannan

2023: Abinda Tinubu Ya Yiwa Borno Lokacin Boko Haram da Babu Wanda Ya Taɓa Mana, Gwamna Zulum

A karshe G-5 Sun Rabu 2, 2 Sun Lamuncewa Tinubu, Gwamnonin Ibo Sun Tsayar da Atiku, Ortom Na Yin Obi

A wani labarin na daban kuma, tawagar G-5 ta fashe gida biyu, kowane ɓangare gmya zaɓi ɗan takarar shugaban ƙasar da zai marawa baya a zaɓen 2023.

Tawagar gwamnonin na G-5 sune waɗanda ke takun saƙa da ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida